Gwamna Ya Zakulo Samari da Zawarawa 300, Zai Masu Auren Gata da Sadakin N250000 a Kebbi

Gwamna Ya Zakulo Samari da Zawarawa 300, Zai Masu Auren Gata da Sadakin N250000 a Kebbi

  • Gwamnatin Kebbi tare da gidauniyar NANAS za su gudanar da bikin gata ga maza da mata 600 (su zama ma’aurata 300) a ranar 27 ga Yuli
  • Gwamna Nasir Idris ya amince da biyan sadakin N250,000 ga kowace amarya tare da kayan ɗaki da kayan abinci ga ma’auratan
  • Bayan an yi gwaje gwaje, marayu da zawarawa da suka cika sharuddan addini da doka daga ƙananan hukumomi 21 ne suka ci gajiyar shirin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kebbi - Gwamnatin Jihar Kebbi tare da haɗin gwiwar gidauniyar Nafisa Nasir (NANAS) sun kammala shirye-shiryen gudanar da auren gata ga ma’aurata 300 a ranar 27 ga watan Yuli.

An bayyana cewa shirin, wanda aka yi wa lakabi da 'auren gata na musamman', ya haɗa da Musulmi da Kiristoci waɗanda suka cika dukkan sharuddan da kwamitin ya gindaya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta gwangwaje iyalan dan sandan da ya mutu a bakin aiki

Gwamnatin Kebbi za ta yi wa maza da mata auren gata a cikin watan Yulin 2026
Wasu mata kenan da aka yi wa auren gata a Gusau, jihar Zamfara. An yi amfani da hoton don misali kawai. Hoto: @KabiruAmadu_MP
Source: Twitter

Za a aurar da marayu, zawarawa

Alhaji Suleiman Argungu, shugaban kwamitin shirya bikin kuma sakataren tsare-tsare na ƙasa na jam'iyyar APC, ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a Birnin Kebbi ranar Talata, in ji rahoton Daily Trust.

Argungu ya ce maza da mata 600 masu shirin aure daga ƙananan hukumomi 21 na jihar ne za su amfana da shirin.

Ya bayyana cewa an zaɓi waɗanda za su ci gajiyar ne daga cikin marayu, zawarawa bayan sun cika dukkan sharuddan addini da na doka da suka shafi aure.

Ya ce wannan shi ne karo na uku da gwamnatin Kebbi ke gudanar da irin wannan shiri, bayan an aurar da mutum 300 a shekarar 2024 da kuma wasu 300 a shekarar 2025.

Gwamnati za ta biya sadaki

Argungu ya ce an kafa kwamitoci daban-daban da suka haɗa da na tsaro, lafiya, sufuri, malamai da kuma gudanarwa domin tabbatar da nasarar shirin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta fara daukar sababbin ma'aikata, matasa 3050 za su samu aiki

Ya ƙara da cewa ana yi wa dukkan masu shirin auren gwaje-gwajen lafiya da suka haɗa da ciki, genotype, HIV/AIDS da sauran sharuddan da doka ta tanada.

A cewarsa, Gwamna Nasir Idris ya amince da biyan sadakin kowace amarya da kuɗi N250,000, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Gwamna Nasir Idris ya ce zai biya sadakin kowace amarya da N250,000
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi na daga hannu ga magoya bayansa. Hoto: @NasiridrisKG
Source: Facebook

Za a ba su kayan ɗaki da abinci

Argungu ya ce gwamnati da abokan haɗin gwiwarta za su kuma bai wa sababbin ma’auratan kayan ɗaki, kayan abinci da sauran kayan amfanin gida domin taimaka musu wajen fara rayuwar aure.

Ya bayyana cewa an ɗauki masu sana'ar ƙera kayan ɗaki na cikin gida domin samar da gadaje, kujerun falo da sauran kayayyakin da za a raba wa waɗanda suka ci gajiyar shirin.

Ya jaddada cewa shirin zai bai wa Musulmi da Kiristoci dama matuƙar sun cika sharuddan da aka tanada, yana mai cewa manufar shirin ita ce ƙarfafa zaman lafiya, ɗabi'un iyali da ci gaban al'umma.

An yi rabon gado da kujeru

Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta rahoto cewa, gwamnatin jihar Kebbi ta yi rabon gado, katifa da kujeru ga amaren da za a aurar a shirin "Auren Gata" na shekarar 2025.

Kara karanta wannan

Shiri ya yi: Yadda fursunoni 61 suka haddace Al Kur'ani mai girma a Kano

Gwamna Nasir Idris ya bayyana cewa ya yi amfani da shirin wajen aurar da mata 300 daga sassa daban-daban na jihar domin rage musu dawainiyar aure.

Kwamishinan labarai, Alhaji Yakubu Ahmed-BK, ya bayyana cewa shirin 'Auren Gata' na shekarar 2025 ya fi wanda aka yi a shekarar 2025 armashi da inganci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com