2027: Atiku Ya Kawo Hujjoji, Ya Zargi Tinubu da Nada Wanda Zai Ruguza 'Yan Adawa a INEC

2027: Atiku Ya Kawo Hujjoji, Ya Zargi Tinubu da Nada Wanda Zai Ruguza 'Yan Adawa a INEC

  • Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya zargi shugaban INEC da ƙoƙarin ruguza jam'iyyun adawa gabanin zaben 2027
  • Atiku ya nuna damuwa kan rade-radin cewa INEC ta ba tsagin ADC na Nafiu Bala lambobin shigar da bayanan yan takara
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi zargin cewa ayyukan INEC karkashin Amupitan na nuna son kai da fifita jam'iyya mai ci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ɗan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi zargi cewa san nada shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, domin ya ruguza yan adawa.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Paul Ibe, ya fitar a madadinsa a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Tofa: Shugaban wata hukuma a Abuja ya ƙi barin ofis duk da Tinubu ya sauya shi

Atiku.
Dan takarar shugaban kasa na ADC, Atiku Abubakar yana magana lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar ADV Global Network a Abuja Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Ya ce idan har zargin da ake yi ya tabbata hakan na nuna cewa INEC ta nuna son kai, kuma matakin na iya haifar da sabon rikici a cikin jam’iyyar ADC gabanin 2027, kamar yadda Punch ta rahoto.

Atiku Abubakar ya yi korafi kan tsarin INEC

Atiku ya yi martani ne bayan shugaban tsagin ADC, Nafiu Bala Gombe, ya sanar cewa ya samu damar loda sunayen 'yan takarar jam’iyyar a manhajar INEC.

A cewarsa, tura sunayen 'yan takara wani muhimmin mataki ne na shirye-shiryen zaɓen 2027, wanda ake yi ne ta hanyar amfani da lambar shiga da INEC ke bai wa jam’iyyun siyasa.

Sai dai Atiku ya ce abin mamaki ne yadda aka bai wa Nafiu Gombe damar amfani da wannan tsarin duk da cewa INEC ta amince da Sanata David Mark a matsayin halastaccen shugaban ADC.

Atiku ya zargi INEC da karya doka

Atiku ya ce:

Kara karanta wannan

Atiku ya fadi abin da Tinubu ya kamata ya yi bayan ceto dalibai 44 a Oyo

“A ranar 11 ga Yulin 2026, Nafiu Bala Gombe, wanda ke ikirarin shi ne shugaban ADC na ƙasa, ya sanar cewa ya yi nasarar loda sunayen 'yan takararsa a manhajar INEC.”
“Ta yaya za a ce akwai shugabanni biyu da INEC ta amince da su a jam’iyya ɗaya? Wannan abu zai yiwu ne kawai a ƙarƙashin INEC da Joash Amupitan ke jagoranta.”

Ya kafa hujja da kundin tsarin mulki

Atiku ya ce Sashe na 222 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) ya tanadi cewa dole ne 'yan takarar jam’iyya su fito ne ta hanyar sahihin zaɓen fidda gwani da INEC ta sa ido a kai.

Amupitan.
Shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan yana jagorantar taro da jam'iyyun adawa a Abuja Hoto: @INECNigeria
Source: Twitter

Ya kuma yi nuni da Sashe na 84 na Dokar Zaɓe ta 2022, wanda ya ce jam’iyya za ta iya gabatar da ɗan takara guda ɗaya kacal ga kowane muƙami.

A ƙarshe, Atiku ya buƙaci INEC ta daina ɗaukar matakan da za su haddasa rikici a cikin jam’iyyun adawa, kamar yadda Daily Post ta kawo.

Gargadin Atiku kan Obi da El-Rufai

A wani labarin, kun ji cewa Atiku Abubakar ya gargadi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu game da jagororin adawa, Peter Obi da Nasir El-Rufa'i.

Kara karanta wannan

'Kar mu ji, kar mu gani': Atiku ya gargadi gwamnati game da Obi, El Rufa'i

Dan takarar shugaban kasa na ADC ya ce kare lafiyar kowane jagoran adawa wajibi ne da kundin tsarin mulki ya ɗora wa gwamnatin Najeriya.

Bisa haka nw Atiku ya ja kunnen gwamnatin tarayya cewa kada ta kuskura ta bari wani abu mara dadi ya samu Peter Obi da Malam Nasir El-Rufai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262