"Ba N27,00 ba": Gwamnatin Tarayya Ta Kara Kudin Jarabawar WAEC, NECO da Kaso 82
- Gwamnatin tarayya ta amince da sabon kudin jarabawar WAEC da NECO na N50,000 daga shekarar 2027
- Sabon kudin jarabawar na NECO da WAEC ya nuna karin kaso 82 idan aka kwatanta da tsohon kudin rajista na N27,500
- Ma'aikatar ilimi ta ce an dauki matakin ne domin a samu daidaitaccen kudin jarabawa tsakanin WAEC da NECO
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta amince da karin kudin jarabawar West African Examinations Council (WAEC) da National Examinations Council (NECO).
Gwamnatin ta amince da karin kudin ne zuwa N50,000 ga kowane ɗalibin sakandare, wanda zai fara aiki daga jarabawar shekarar 2027.

Source: Twitter
Jaridar TheCable ta kawo rahoton cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan kula da manyan makarantun sakandare na ma'aikatar ilimi, Adeniji Ibrahim, ya fitar a ranar 18 ga Yuni.
Sanarwar ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan bukatar da WAEC ta gabatar na a sake duba kudin rajistar jarabawar Senior School Certificate Examination (SSCE) daga shekarar 2027.
An kara kudin jarabawa da kaso 82
A baya, kudin rajistar jarabawar ya kasance N27,500, wanda ke nufin sabon kudin N50,000 ya nuna karin kusan kaso 82.
Adeniji Ibrahim ya ce an cimma wannan matsaya ne bayan taron da Ministan ilimi ya yi da hukumomin shirya jarabawa a ranar 31 ga Maris, 2026, inda aka tattauna bukatar sake duba kudaden gudanar da jarabawa.
A cewarsa, Ministan ya umarci WAEC da NECO su rika amfani da kudin rajista iri daya wajen gudanar da jarabawar SSCE.
Sanarwar ta ce:
"Za ku tuna cewa a taron hukumomin shirya jarabawa da aka gudanar tare da mai girma Ministan ilimi a ranar 31 ga Maris, 2026, an tattauna bukatar sake duba kudaden jarabawa. Bayan haka, ministan ya umarci WAEC da NECO su yi amfani da daidaitaccen kudin rajista wajen gudanar da jarabawar SSCE."
"Saboda haka, an umurce ni da na isar da amincewar mai girma Ministan ilimi kan sabon kudin jarabawa na N50,000 ga kowane ɗalibi, wanda zai fara aiki daga jarabawar NECO SSCE (Internal) ta shekarar 2027."
Ma'aikatar ilimin ta bukaci a sanar da dukkan masu ruwa da tsaki game da wannan sabon tsari domin su dauki matakan da suka dace kafin fara aiwatar da shi.

Source: Twitter
Ma'aikatar ilimi ta tabbatar da amincewar
Da take tabbatar da labarin a ranar Asabar, 11 ga watan Yulin 2026, daraktar yada labarai da hulda da jama'a ta ma'aikatar ilimi, Folasade Boriowo, ta ce gwamnatin tarayya ta amince da karin kudin jarabawar.
"Zan iya tabbatar da cewa an amince da karin kudin jarabawar. Na yi magana da daraktan da ke kula da wannan bangare mintuna kadan da suka gabata, kuma ya tabbatar mini cewa an ba da wannan amincewa."
- Folasade Boriowo
Fursunoni sun zana jarabawar NECO
A wani labarin kuma, kun ji cewa Hukumar kula da fursunoni ta Najeriya, reshen Jihar Kano, ta bayyana cewa wasu daga cikin daurarrua Kano sun yi fice a NECO.
A cikin sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce fursunoni 68 sun yi nasara a jarabawar kammala sakandare ta NECO a bana.
Asali: Legit.ng

