Kano: Majalisa Ta Yi Sabuwar Doka, za a Kayyade Kuɗin Makarantu Masu Zaman Kansu
- Majalisar Dokokin Kano ta amince da dokar da za ta takaita yadda makarantu masu zaman kansu ke ƙara kuɗin makaranta a faɗin jihar
- Sabuwar dokar ta wajabta wa makarantu tuntubar ƙungiyar iyaye da malamai (PTA) kafin ƙara kuɗi, kuma ƙarin ba zai wuce kashi 10 ba
- Dokar ta kuma rage kuɗin harajin da makarantu ke biya ga Hukumar Makarantu Masu Zaman Kansu daga kashi 15 zuwa kashi 5
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Kano - Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da wata doka da za ta tsara yadda makarantu masu zaman kansu ke ƙara kuɗin makaranta a faɗin jihar.
Dokar mai taken 'Kano State Private and Voluntary Institutions Board (Amendment) Bill, 2026', ta ƙunshi matakan da za su ƙarfafa sa ido kan ayyukan makarantu masu zaman kansu tare da kare iyaye daga ƙarin kuɗin makaranta ba bisa ƙa'ida ba.

Source: Facebook
An yi dokar kudin makarantu a Kano
Majalisar ta amince da dokar ne bayan karatu na uku da Magatakardar Majalisar, Bashir Diso, ya yi, sannan aka tattauna ta a Kwamitin Majalisa gaba ɗaya yayin zaman majalisar, in ji rahoton Premium Times.
Da yake magana bayan amincewa da dokar, Jagoran Masu Rinjaye na Majalisar, Lawan Hussaini, ya bayyana cewa dokar ta wajabta wa makarantu masu zaman kansu na firamare da sakandare tuntubar ƙungiyar Iyaye da Malamai (PTA) kafin su ƙara kuɗin makaranta.
Ya ce dokar ta kuma tanadi cewa duk wani ƙarin kuɗin makaranta da aka amince da shi ba zai wuce kashi 10 cikin ɗari na kuɗin makarantar da ake bi a halin yanzu ba.
An kayyade kudin jarabawar makarantu
Bugu da ƙari, dokar ta tanadi cewa mukamin Babban Sakataren Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu da Na Sa-kai zai kasance na gogaggen malami ko wanda ya yi ritaya daga aikin gwamnati, kuma ya kai aƙalla mataki na 14 (Grade Level 14).
Hussaini ya ƙara da cewa dokar ta haramta wa makarantu karɓar kuɗin rijistar jarrabawa fiye da kashi 10 cikin ɗari sama da kuɗin da hukumomin jarrabawa irin su WAEC, NECO da NBTE suka kayyade.
Ana jiran amincewar gwamnan Kano
Har ila yau, FRCN ta rahoto cewa dokar ta rage kuɗin da makarantu masu zaman kansu ke biya Hukumar daga kashi 15 cikin ɗari zuwa kashi biyar cikin ɗari.

Source: Facebook
A cewarsa, waɗannan gyare-gyare na daga cikin matakan da gwamnati ke ɗauka domin inganta tsarin gudanarwa da kuma ɗaga darajar ilimi a faɗin Jihar Kano.
Dokar dai na jiran sahalewar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, kafin ta fara aiki.
An gyara makarantu masu yawa a Kano
A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Kano ta bayyana cewa tana kan bakarta na tabbatar da dawo da martabar ilimi a dukkanin sassan jihar.
Gwamnati ta ce zuwa yanzu, ta gyara fiye da makarantu 1,200 a ƙananan hukumomi 44, bayan haka kuma ta yi gyara a sassan Kano.
Haka kuma ta ware N3bn don gyaran makarantu 13 na ’yan mata da aka rufe a baya, a wani yunkuri na dawo da darajar ilimi a jihar.
Asali: Legit.ng

