Darussan da Marigayi Buhari Ya Koya wa Ƴaƴansa Lokacin da Yake Raye
- Yar marigayi Muhammadu Buhari ta bayyana kyawawan halayen tsohon shugaban kasar Najeriya
- Hanan Buhari ta ce marigayi mahaifinta, Buhari, ya koya mata muhimmancin gaskiya, juriya da hidimar al'umma,
- Ta bayyana haka ne bayan karɓar lambar yabo a taron shugabanci da kasuwanci da aka gudanar a Morocco
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Marrakech, Morocco - Hanan Buhari, 'yar marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ta tuna kyawawan halayen mahaifinta.
Hanan ta ce mahaifinta ya koya mata darussan riko da gaskiya, juriya da hidimar jama'a ba tare da son kai ba.

Source: Twitter
Hanan ta yi wannan bayani ne a birnin Marrakech na ƙasar Morocco bayan karɓar lambar yabo ta 100 Most Notable Peace Icons of Africa, cewar The Nation.
Hanan Buhari ta karrama marigayi mahaifinta

Kara karanta wannan
2027: Malami ya gana da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a Abuja
A wata sanarwa da Daraktan aikin taron, Kingsley Amafibe, ya fitar, Hanan ta sadaukar da wannan lambar yabo ga marigayi mahaifinta cikin alhini.
Ta bayyana cewa irin tarbiyyar, horo da amincewar da mahaifinta ya nuna mata ne suka taimaka wajen gina rayuwarta da kuma ƙarfafa mata gwiwar cimma buri.
Ta ce:
"Na sadaukar da wannan karramawa ga marigayi mahaifina, Shugaba Muhammadu Buhari, wanda shawararsa, horonsa da amincewarsa da ni suka gina macen da na zama.
"Ya koya min muhimmancin gaskiya, juriya da hidimar al'umma ba tare da son kai ba. Amincewarsa da ni ta ba ni ƙarfin gwiwar yarda da kaina."

Source: Instagram
Alwashin da Hanan Buhari ta sha kan mahaifinta
Hanan ta ce za ta ci gaba da kare ƙa'idojin da mahaifinta ya koyar da ita ta hanyar ƙarfafa mata da kuma bayar da gudunmawa mai amfani ga al'umma.
Amafibe ya taya Hanan Buhari murnar wannan karramawa, yana mai bayyana ta a matsayin abin koyi da ke ƙarfafa sabon ƙarni na shugabannin Afirka.
Ya ce jajircewarta wajen bunƙasa rayuwar mata na ci gaba da zaburar da matasa da dama a nahiyar wajen neman shugabanci nagari da ci gaba, cewar Punch.
An shirya taron ne ƙarƙashin gidauniyar DAVDAN Peace and Advocacy Foundation da 100 Most Notable Peace Icons Africa tare da halartar shugabanni da 'yan kasuwa.
Haka kuma masu tsara manufofi, jami'an diflomasiyya da sauran manyan baƙi daga sassa daban-daban na Afirka sun halarci taron domin karrama fitattun mutane.
Taron ya mayar da hankali ne kan yabawa waɗanda suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen shugabanci, samar da zaman lafiya, kasuwanci da bunƙasa ci gaba mai ɗorewa a nahiyar.
Haka kuma masu tsara manufofi, jami'an diflomasiyya da sauran manyan baƙi daga sassa daban-daban na Afirka sun halarci taron domin karrama fitattun mutane.
Yadda Hanan ta bude Gidauniya a Kaduna
A baya, an ji cewa Hanan Buhari, daya daga cikin 'yayan shugaba Muhammadu Buhari ta yi Alla-wadai da yadda ake fyade a Najeriya.
Hanan ta kaddamar da sabuwar gidauniyar kare hakkin yara da mata da ake cin zarafi a Najeriya wanda ya ke daya daga cikin matsalolin da ake fama da su.
Yar marigayi Muhammadu Buhari tana auren Muhammad Turad Sha'aban, 'dan tsohon dan takaran kujerar gwamnan jihar Kaduna.
Asali: Legit.ng
