Aisha Buhari: 'Manyan Abubuwa 2 da Tsohon Shugaban Ƙasa Ya Bari a Najeriya '
- Hajiya Aisha Buhari ta ce bayyana wasu daga cikin manyan abubuwan da tsohon sh yi shugaban kasa ya gadar wa Najeriya
- Ta fadi wannan ne bayan ta fara aikin gina sabon rukunin kwalejin kimiyyar kwamfuta a Jami'ar Al-Qalam da ke Katsina daga kuɗin littafin tarihin Buhari
- An ƙaddamar da aikin a gaban jami'an gwamnatin jihar Katsina da shugabannin jami'ar inda suka yaba wa iyalan Buhari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Katsina–Tsohuwar matar shugaban ƙasa, Hajiya Aisha Muhammadu Buhari, ta bayyana mafi girman gadon da marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya bari shi a Najeriya .
Ta bayyana cewa daga cikin abubuwan da tsohon shugaban ya bari akwai jajircewarsa wajen bunƙasa ilimi da haɓaka ƙwarewar al'umma.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta wallafa cewa Aisha Buhari ta bayyana haka ne a ranar Lahadi 5 ga watan Yuli, 2026 yayin da ta ƙaddamar da fara aikin gina sabon rukunin Kwalejin Kimiyyar Kwamfuta a Jami'ar Al-Qalam da ke jihar Katsina.
Aisha Buhari ta kaddamar da aiki a Katsina
Arise News ta ruwaito za a aiwatar da aikin ne da kuɗin da aka samu daga sayar da littafin 'From Soldier to Statesman: The Legacy of Muhammadu Buhari.'
Da take jawabi ga manyan baƙi da suka halarci taron, Aisha Buhari ta ce aikin wata alama ce ta ƙudirin iyalan Buhari na ci gaba da raya tarihinsa.
Ta ce:
"Yau ba kawai muna fara gina sabon gini ba ne, muna fara wani hangen nesa da zai ba matasa ilimi da ƙwarewar da za su buƙata domin cin gajiyar duniyar zamani mai tafiya da fasahar dijital."
Za a rika tuna wa da Buhari
Aisha Buhari ta ƙara da cewa sabon rukunin zai kasance abin tunawa mai ɗorewa ga marigayi Buhari, wanda rayuwarsa ta ta'allaka ne kan aiki tukuru, ladabi, gaskiya da sadaukar da kai wajen ci gaban Najeriya.
A cewarta, mafi kyawun abin tunawa da mutum zai iya bari ba ginin siminti ba ne, illa cibiyar da za ta reni ilimi, tarbiyya da damar ci gaba ga al'ummomi masu zuwa.

Source: Facebook
Aisha Buhari ta kuma jaddada cewa ƙasashen da suka fi mayar da hankali kan kimiyyar kwamfuta, fasahar AI, tsaron yanar gizo, injiniyoyin manhajoji da kirkire-kirkiren fasaha su ne za su jagoranci ci gaban duniya a nan gaba.
A jawabin gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, wanda mataimakinsa Faruk Lawal Jobe ya wakilta, ya yabawa iyalan Buhari bisa ci gaba da raya manufofin marigayin ta hanyar tallafa wa ilimi.
Za a yi bikin tuna Buhari
A baya, kun ji cewa tsohon shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya kusa cika shekara daya da rasuwa bayan jinyar da ya yi a birnin London a shekarar 2025.
Biyo bayan haka, 'yan uwa da abokan arziki sun shirya wani taro na musamman domin tunawa da tsohon shugaban kasar Shugaba Muhammadu a Najeriya.
Buhari ya rasu ne bayan yar gajeriyar jinya da ta kama shi bayan ya kammala mulkin Najeriya na shekara takwas da ya yi tsakanin 2015 zuwa 2023.
Asali: Legit.ng


