'Yan Bindiga: Kungiyar Duniya Ta Yi Wuf Ta Yi Magana da Jin An Cafke Malami a Katsina
- Amnesty International ta yi maza ta fitar da jawabi da jin labarin cewa an yi ram da Dr. Bashir Kurfi a ranar Laraba
- Kungiyar mai fafutukar kare hakkin al’umma a duniya ta ce hukuma tana so a rike malamin kuma babu ranar sakin shi
- Jawabin Amnesty ya nuna an cafke Dr. Kurfi ne saboda ya soki manufofin gwamnati wajen yaki da ‘yan bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Katsina – Kungiyar nan ta Amnesty International mai kare hakkin Bil Adama a duniya ta yi Allah-wadai da cafke Bashir Kurfi da aka yi.
Amnesty International ta bayyana kama malamin jami’ar a matsayin kokarin yaki da ‘yancin albarkar bakin da dokar kasa ta ba kowane mutum.

Source: Facebook
Kungiyar Amnesty Int'l ta soki kama Bashir Kurfi
A wani jawabi da ta fitar a ranar Laraba a shafin Facebook, kungiyar ta ce hukuma tana kokarin tsare Dr. Bashir Kurfi har sai illa Ma shaa Allahu.

Kara karanta wannan
ICPC: Jam'iyyar ADC ta jero bukata 6 da ta yi maganar mugun halin da El Rufai ke ciki
Amnesty Int’l ta yi zargin cewa ana so a yi amfani da kotuna da jami’an ‘yan sanda wajen cigaba da garkame Kurfi, a hana shi samun ‘yanci.
Jawabin kungiyar ya nuna za a fake da wasu tuhume-tuhume na bogi wajen tsare shi, abin da ta kira kokarin hana ‘yancin tofa albarkarcin baki.
Amnesty ta ce babu ranar sakin Dr. Kurfi
Daily Trust ta rahoto kungiyar tana cewa abin da gwamnatin jihar Katsina ta ke so shi ne hana mutane yin magana game da lamarin ‘yan bindiga.
An shafe shekara da shekaru ‘yan bindiga suna hallaka bayin Allah musamman a kauyukan Katsina.
“Bai kamata a azabtar da wani saboda ya soki gwamnati ko ya binciki ayyukan gwamnati ba,
Dr. Bashir Kurfi bai aikata laifin komai ba, kama shi ya nuna giyar mulki baro-baro. Yana da ‘yancin da za iyi tambayoyi ko ya soki manufofin gwamnati.
- Amnesty Int'l
Gwamnatin jihar Katsina da dakarun ‘yan sanda ba su tanka maganar da kungiyar duniyar ta yi ba.
Tsohon hadimin gwamna ya kare kama Kurfi
Amma da yammacin Laraba, an ga Shugaban karamar hukumar Katsina, Hon. Isa Miqdad yana tofa albarkacin bakinsa game da lamarin a shafinsa.
Hon. Isa Miqdad ya maida wa wani martani da ya ji yana zargin Gwamna Dikko Radda da cafke babban malamin jami’ar ta ABU kuma ‘dan kasuwa.
Tsohon hadimin na gwamnan Katsina ya kare Mai girma Dikko Radda a kafar X, ya ce abin da ake bukata kawai shi ne Kurfi ya gabatar da hujjojinsa.
“Dakta ya kawo hujjojinsa kawai, shikenan”
- Isah Miqdad
Jama’a sun shiga maida wa matashin ‘dan siyasar da amsa, ana zargin Gwamnatin Katsina da iya kama malamin amma ba a cafko ‘yan bindiga ba.
Wani mai suna Mr. Muslim ya tuna masa cewa an kama wadanda ake zargin ‘yan bindiga ne daga cikin mahajjatan da suka sauke farali ta Katsina.
Kotu ta rufe Dr. Bashir Kurfi a Katsina
An gurfanar da Bashir Kurfi a gaban kotu ne kan zargin da ya yi cewa Gwamnatin Katsina ta ɗauki nauyin tura wasu 'yan bindiga aikin hajjin 2026.
Kamar yadda aka ji labari a tsakiyar makon nan, Kotu ta umurci a tsare malamin jami'a Dr. Bashir Kurfi da ake zargi da ɓata sunan Gwamnatin Katsina.
Bayan da aka karanta masa tuhume-tuhumen da ake masa a gaban kotu, Dr. Kurfi ya musanta dukkan zarge-zargen, sai aka daga sauraron kara.
Asali: Legit.ng

