Asirin Matar Aure Ya Tonu, An Gano Tana Sheke Aya a Otal bayan an Tara N20m Kudin Fansa

Asirin Matar Aure Ya Tonu, An Gano Tana Sheke Aya a Otal bayan an Tara N20m Kudin Fansa

  • Wata mata da aka bayyana sunanta da Oluchi, wadda iyalanta suka ce an yi garkuwa da ita a Edo, ta shiga komar 'yan sanda bayan an gano ta shirga 'karya
  • Jami'an tsaro sun gano matar tare da saurayinta a wani otal da ke jihar Delta bayan ta jefa mijinta, yara da sauran 'yan uwa a cikin mawuyacin halin nemo kudin fansa
  • Iyalanta sun yi ta neman tallafin kuɗin fansa bayan masu garkuwar sun nemi Naira miliyan 50 kafin daga baya suka sassauto domin a sako Oluchi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Delta – Wata mata mai suna Oluchi, wadda iyalanta suka bayyana cewa an yi garkuwa da ita a jihar Edo, ta shiga hannun jami'an tsaro.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: An hallaka mawaki dan asalin Najeriya a Burtaniya

Jami'an rundunar 'yan sanda sun gano Oluchi tana duniyanci tare da wani da ake zargin saurayinta ne a wani otal da ke jihar Delta.

Yan sanda su gano matar aure da wani a otal
Wasu daga cikin jami'an tsaro a bakin aiki Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa lamarin ya zo ne bayan danginta da abokanta sun shafe kwanaki suna kokarin tara kuɗin fansa domin ceto ta daga hannun masu garkuwa da mutane.

An kai korafin yin garkuwa da matar aure

Rahoton jaridar Punch ya bayyana cewa tun da farko, iyalan matar sun kai rahoto ga rundunar 'yan sanda cewa an yi garkuwa da ita ne a yankin Ikpoba Hill da ke ƙaramar hukumar Ikpoba-Okha a jihar Edo.

'Ya'yanta, daga ciki har da wata diyarta mai suna Anita da ke zaune a ƙasar Canada, sun roƙi jama'a da su taimaka wajen tara kuɗi bayan masu garkuwar sun bukaci Naira miliyan 50 a matsayin fansa.

Sai dai bayan an yi ciniki tare da ba su baki, wadannan masu garkuwa da mutane sun rage yawan kudin da za a biya zuwa Naira miliyan 20.

Yadda aka kama matar auren da aka 'sace'

Kara karanta wannan

Babu zancen shari'ar Musulunci: Ƴan bindiga da suka sace dalibai a Oyo sun fadi bukatunsu

Rahotanni sun nuna cewa binciken da jami'an 'yan sanda suka gudanar ya kai su wani otal da ke Ubiaroko a jihar Delta, a nan suka gano matar tare da wani mutum.

Wata majiya da ke da masaniya kan binciken ta bayyana cewa jami'an tsaro sun bi diddigin wata lambar waya da ake alakantawa da ɗaya daga cikin wadanda ake zargi har zuwa otal ɗin.

Yan sanda sun gano matar a jihar Delta
Taswirar jihar Delta, inda aka ga matar aure da abin kunya a otal Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ta ce:

"Jami'an 'yan sanda sun bi sawun lambar wayar mutumin zuwa wani otel a Ubiaroko, jihar Delta. A can suka tarar da mutumin da matar da aka ce an yi garkuwa da ita suna tare a cikin otal."

Majiyar ta kara da cewa bayan gano hakan ne aka sanar da mijin matar game da abin da aka gano, yayin da ake ci gaba da bincike.

Da take mayar da martani, Anita ta bayyana cewa za su mayar da duk kuɗin da aka tara bayan sun fahimci cewa ba ainihin garkuwa da mutane aka yi da ita ba.

A cewarta, masu bincike sun sanar da su cewa mahaifiyarta da mutumin da aka gano tare da ita sun yi wata yarjejeniya domin samun wani kaso daga cikin kuɗin da aka tara.

Kara karanta wannan

Sababbin bayanai sun fito kan sace ƙanwar tsohon minista Adelabu a Oyo

A halin yanzu, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Edo, CSP Moses Yamu, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa an kama mutum huɗu da ake da alaƙa da batun, yayin da bincike ke ci gaba.

An tarwatsa masu garkuwa da mutane

A wani labarin, kun ji cewa jami’an tsaron dararen hula, NSCDC sun fafata da wasu ƴan bindiga da suka yi yunkurin kai hari ƙaramar hukumar Kiru a jihar Kano bayan sun samu kiran gaggawa.

Maharan sun jikkata wani makiyayi tare da sace ‘ya’yansa biyu kafin jami’an tsaro su fatattake su, inda aka tabbatar da cewa sun tsere da raunuka daban daban zuwa cikin dazukan dake kusa.

Jami'an hukumar NDC sun yi nasarar ceto yaran bayan an yi zazzafan dauki ba dade tare da nuna masu ƙarfin makami da kwarewar aiki, tare da neman goyon baya da hadin kai wajen kare rayuka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng