Yadda Aka Kashe Mutane 792 a Borno, Zamfara, Neja da Wasu Jihohi a Wata 1 kacal

Yadda Aka Kashe Mutane 792 a Borno, Zamfara, Neja da Wasu Jihohi a Wata 1 kacal

  • Rahoton SARI Global ya nuna cewa mutane 792 sun mutu a hare-hare 882 da suka afku a dukkan jihohin Najeriya da Abuja cikin Yunin 2026
  • Rahoton ya ce dakarun sojoji sun kashe 'yan ta'adda 274, yayin da ISWAP ta tsananta hare-hare kan ayyukan agajin jin kai a Borno
  • Borno ce ta fi fama da hare-haren 'yan ta'adda, in da aka kashe mutum 172, sai Zamfara, Plateau, Katsina, Lagos, Abuja, Rivers da sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Rahoton wani kamfanin nazarin tsaro, SARI Global, ya bayyana cewa akalla mutane 792 ne suka rasa rayukansu a hare-haren 'yan ta'adda 882 da suka faru a jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja cikin watan Yunin 2026.

Rahoton ya kuma nuna cewa dakarun sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda 274 a wannan lokaci, yayin da kungiyar ISWAP ta kara tsananta hare-hare a yankin Monguno na jihar Borno tare da hana kayan agajin jin kai isa ga dubban 'yan gudun hijira.

Kara karanta wannan

Yadda musayar wuta tsakanin sojoji da Boko Haram ya yi ajalin amarya a Borno

Rahoto ya nuna cewa an kashe mutane 792 a watan Yunin 2026
Dakarun sojojin Najeriya suna tafiya a kan tankar yaki a cikin daji. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Rahoton tsaron Najeriya a Yunin 2026

Legit Hausa ta fahimci cewa rahoton na da taken 'nazari kan tsaron Najeriya a cikin watan Yunin 2026,' kuma wallafa shi ne a shafin ReliefWeb na Majalisar Dinkin Duniya.

Rahoton nuna cewa mako na biyu na watan ne ya fi muni, inda aka samu hare-hare 278 tare da mafi yawan mace-mace.

An kuma bayyana cewa ranakun 8, 11, 13 da 14 ga watan Yunin sun kasance mafi tashin hankali saboda hare-haren 'yan ta'adda, 'yan bindiga da kuma samemen jami'an tsaro.

ISWAP ta tsananta hare-hare a Borno

Rahoton ya bayyana cewa babban abin da ya fi daukar hankali shi ne yadda mayakan ISWAP suka kai farmaki a yankin rukunin gidaje 20 da ke Monguno a ranar 24 ga Yuni, inda suka sace wani ma'aikacin wata kungiya mai zaman kanta ta kasa da kasa da kuma mai gadinsa.

Bayan haka kuma sun kona manyan motocin daukar kayan agaji a hanyar Monguno zuwa Gajiram domin dakile kai kayan taimako ga sansanonin 'yan gudun hijira.

Kara karanta wannan

Sojoji sun samu gagarumar nasara bayan kashe manyan yan ta'adda 8 a Katsina

Jihohin da aka fi kashe mutane

A cewar rahoton, jihar Borno ce ta fi kowace jiha fama da matsalar tsaro, inda aka samu hare-hare 109 da kuma mutuwar mutane 172.

Jihar Borno ce ta fi fama da matsalar tsaro a Najeriya a watan Yunin 2026.
Taswirar jihar Borno, inda aka kashe mutane 172 a watan Yunin 2026. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Zamfara ta biyo baya da hare-hare 63, sai Plateau mai 51, Katsina 44, Lagos 40, FCT Abuja 36, Rivers 32, yayin da Oyo da Sokoto suka samu 31 kowacce, sannan Niger ta samu hare-hare 29.

Rahoton ya raba adadin mace-macen zuwa rukuni daban-daban, inda ya nuna cewa jami'an gwamnati sun kashe mutane 274, 'yan kungiyoyin masu dauke da makamai 337 sun mutu, sannan fararen hula 64 suka rasa rayukansu.

Hakakuma, 'yan ta'adda 30 suka mutu, mutane 86 suka mutu a hare-haren da ba a tantance masu aikata su ba, yayin da mutum daya ya mutu a rikicin siyasa.

Jiragen soji sun farwa taron 'yan bindiga

A wani labari, mun ruwaito cewa, Dakarun Operation Fansan Yamma sun dakile hare-haren da ake zargin 'yan bindiga ne suka shirya a Zamfara.

Kara karanta wannan

Kotu ta umarci a tsare malamin jami'ar ABU saboda kalaman da ya yi kan gwamnatin Katsina

Haka kuma, dakarun sojojin sun kashe wani fitaccen kwamandan 'yan bindiga tare da tarwatsa wani shirin kai babban hari ta hanyar luguden wuta daga sama.

Rundunar sojin sama ta kuma sanar da kai farmaki kan 'yan bindiga kusan 300 da ke kan babura, inda suka kashe da dama daga cikinsu a Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com