Kotu Ta Umarci a Tsare Malamin Jami'ar ABU saboda Kalaman da Ya Yi kan Gwamnatin Katsina
- Kotun Majistare da ke jihar Katsina ta ba da umarnin tsare malamin jami'a, Dr. Bashir Kurfi a hannun 'yan sanda kafin zama na gaba
- An gurfanar da malamin ne a gaban kotu bayan ya fito ya yi iƙirrin cewa gwamnatin Katsina ta tura 'yan bindiga aikin hajji
- Dr. Kurfi ya musanta zargin bayan an karanta masa tuhume-tuhume, inda daga bisani kotu ta ɗage sauraron shari'ar zuwa 14 ga Yulin 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Wata Kotun Majistare da ke jihar Katsina ta bayar da umarnin tsare Dr. Bashir Kurfi, malami a jami'a kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, a hannun 'yan sanda.
Alƙalin kotun, Mai Shari'a Zaharaddeen Kofar Soro, ne ya bada umarnin bayan Rundunar 'Yan Sandan Jihar Katsina ta gurfanar da Dr. Kurfi bisa zargin bata suna da kuma yaɗa labaran ƙarya.

Source: Facebook
Dalilin gurfanar da Bashir Kurfi a kotu
Daily Trust ta ce Rahoton Farko na Shari'a (FIR) ya nuna ana zargin Dr. Kurfi, wanda malami ne a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, da yin kalaman da suka bata sunan gwamnatin Katsina.
Bayanai sun nuna cewa malamin ya shiga wannan matsala bayan ya zargi gwamnatin Katsina da daukar nauyin wasu yan bindiga zuwa aikin hajji.
'Yan sanda sun gurfanar da shi bisa tuhume-tuhume biyu ƙarƙashin Sashe na 308 da 309(1) na Dokar Penal Code ta jihar Katsina.
Masu gabatar da ƙara sun ce Dr. Kurfi ya yi zargin gwamnatin Katsina ta ɗauki nauyin aikin Hajji shugabannin 'yan bindiga, zargin da suka bayyana a matsayin ƙarya, mai mugun nufi kuma wanda zai iya ɓata martabar gwamnati da al'ummar jihar.
Dr. Bashir Kurfi ya musanta zargi
Masu gabatar da ƙarar sun kuma ce wanda ake zargin ya yi wannan furuci ne yana sane ko kuma yana da dalilin sanin cewa zai cutar da mutuncin gwamnati da jama'ar Katsina.
Bayan an karanta masa tuhume-tuhumen, Dr. Kurfi ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa, kamar yadda Vanguard ta kawo.
Daga nan ne masu gabatar da ƙarar suka roƙi kotu da ta ci gaba da tsare shi a hannun 'yan sanda har sai an kammala bincike, suna masu cewa sakinsa da beli a wannan mataki na iya kawo cikas ga binciken.
Sai dai lauyan wanda ake ƙara, A.D. Umar, ya buƙaci kotun ta ba wanda yake karewa beli, yana mai cewa yana da haƙƙin kasancewa cikin 'yanci yayin da ake ci gaba da shari'ar.

Source: Facebook
An ɗage shari'ar zuwa 14 ga Yuli
Alƙalin kotun ya umarci 'yan sanda su ci gaba da bincike tare da bayar da umarnin ci gaba da tsare Dr. Kurfi a hannunsu har zuwa ranar da za a dawo shari'ar.
Bayan haka, kotun ta ɗage ci gaba da sauraron ƙarar zuwa ranar Litinin, 14 ga Yulin 2026.
Gwamnatin Katsina ta karyata Bashir Kurfi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Katsina ta yi martani kan zargin cewa ta dauki nauyin kai wasu 'yan bindiga zuwa aikin Hajji.

Kara karanta wannan
Mutanen da 'yan bindiga suka sace a wurin Ibada sun dawo gida, mutum 1 ya mutu a Ekiti
Gwamnatin ta yi watsi da zargin cewa ta ɗauki nauyin aikin hajjin wasu 'yan bindiga, inda ta bayyana iƙirarin a matsayin na ƙarya.
Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, Nasir Mu’azu, ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar bayan kamalan Dr. Bashir Kurfi.
Asali: Legit.ng

