Sojoji Sun Gano Wasu Ƴan Ta'addan Ƙasashen Waje a Borno, Sun Karya Lagon ISWAP

Sojoji Sun Gano Wasu Ƴan Ta'addan Ƙasashen Waje a Borno, Sun Karya Lagon ISWAP

  • Sojoji sun ce sun kashe mai ɗaukar bidiyon ISWAP tare da ƙwato kyamara da ke dauke da wasu muhimman bayanai game da 'yan ta'addan a Borno
  • Binciken farko ya ba sojoji damar gano bayanan wasu ƙwararrun ƴan ta'adda daga ƙasashen waje da le taimaka wa kungiyar ISWAP
  • Rundunar ta ce an kashe mai daukar bidiyon da tarwatsa lagon ISWAP ne a harin da suka kai dpn sace magungunan cutar kwalara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Borno - Dakarun Operation Hadin Kai sun ce sun dakile wani yunƙurin harin mayaƙan ƙungiyar ISWAP a yankin Cross Kauwa da ke ƙaramar hukumar Kukawa a jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa sojojin sun samu nasarar kashe mai ɗaukar bidiyon ƙungiyar ISWAP din tare da ƙwato kyamarar bidiyo mai ɗauke da bayanan sirri.

Kara karanta wannan

Cuta ta barke a sansanin 'yan ta'addan ISWAP, mayaka da dama sun mutu a Borno

Sojoji sun kashe mai daukar hoto da bidiyon ISWAP
Wasu hotunan 'yan ta'addan kasashe waje da aka gani a kyamar mai daukar bidiyon ISWAP da sojoji suka kama a Borno. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Sojoji sun dakile harin ISWAP

Mai riƙon muƙamin jami'in yaɗa labaran rundunar, Kyaftin Muhammed Goni, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, kamar yadda ZagazOla Makama ya wallafa a shafinsa na X.

A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:20 na daren Asabar, lokacin da mayaƙan ISWAP suka yi yunƙurin kai hari kan sansanin sojoji domin sace kayayyakin maganin cutar kwalara.

Rundunar ta ce jami'anta sun gano motsin mayaƙan tun kafin su kai ga cimma manufarsu, inda suka buɗe musu wuta mai ƙarfi.

Ta ce hakan ya tilasta wa mayaƙan tserewa daga wurin, bayan sun yi asarar mutane da dama.

Bayan artabun, dakarun sun ƙwato kyamarar bidiyo ta Sony, harsasai, kayan yaƙi da wasu kayayyakin mayaƙan ƙungiyar.

Bayanai kan ƙwararrun ƴan ta'adda daga waje

Rundunar ta ce binciken farko da aka gudanar kan bidiyon da ke cikin kyamarar ya nuna cewa hare-haren ISWAP na samun jagoranci daga manyan kwamandoji huɗu tare da taimakon wasu ƙwararrun mayaƙa uku daga ƙasashen waje.

Kara karanta wannan

An gwabza fada tsakanin sojoji da Boko Haram, an kona wurare a Borno

A cewar sanarwar, an bayyana ɗaya daga cikinsu a matsayin Abu Ishaq, wanda aka ce ɗan ƙasar Falasɗinu ne kuma babban mai horas da mayaƙan ISWAP.

Haka kuma, an bayyana wani mai suna Abu Thaiba, wanda aka ce ɗan ƙasar Morocco ne kuma likitan ƙungiyar.

Rundunar ta ce an kuma gano wani ɗan yankin Larabawa na uku, sai dai har yanzu ba a tantance ƙasar da ya fito ba, in ji rahoton Daily Post.

Sai dai Legit Hausa ba ta iya tabbatar da waɗannan ikirari daga wata majiya mai zaman kanta ba, kuma babu wata sanarwa daga ISWAP da ta mayar da martani kan zargin.

An ce 'yan ta'addan sun yi yunkurin farmakar sansanin sojoji don sace kayayyaki
Taswirar jihar Borno inda aka kashe mai daukar bidyon mayakn ISWAP. Hoto: Legit,ng
Source: Original

Wani dalilin mayaƙan na kai hari

Operation Hadin Kai ta ce bayanan sirrin da aka samu sun nuna yiwuwar barkewar cutar kwalara a sansanonin ISWAP, wanda hakan ne ya sa mayaƙan suka yi yunƙurin sace magungunan cutar daga sansanin sojoji.

Sanarwar ta ƙara da cewa hotunan tauraron ɗan adam da bayanan sirri sun nuna cewa mayaƙan sun kwashe gawarwakin wasu daga cikin waɗanda aka kashe tare da janye waɗanda suka jikkata daga wurin artabun.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai hari a Sokoto, an kashe mutane da jikkata wasu

Rundunar ta bayyana cewa sojoji biyu sun samu raunukan harbin bindiga yayin musayar wutar, amma an garzaya da su ta jirgin sama zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com