Nasara daga Allah: Jiragen Sojoji Sun Far Wa Taron 'Yan Bindiga 300 a Jihar Zamfara

Nasara daga Allah: Jiragen Sojoji Sun Far Wa Taron 'Yan Bindiga 300 a Jihar Zamfara

  • Dakarun rundunar sojoji ta Operation Fansan Yamma sun dakile hare-haren 'yan bindiga a Kaura Namoda da ke jihar Zamfara
  • Jami'an tsaron sun yi nasarar kashe Alhaji Tukur, kani ga fitaccen shugaban 'yan bindiga Alhaji Shehu Bagiwaye
  • Rundunar sojin sama ta kai farmaki kan 'yan bindiga kusan 300 da ke kan babura, inda suka kashe da dama daga cikinsu a Zamfara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - Dakarun Rundunar Hadin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, wato Operation Fansan Yamma sun dakile hare-haren da ake zargin 'yan bindiga ne suka shirya a Zamfara.

Haka kuma, dakarun sojojin sun kashe wani fitaccen kwamandan 'yan bindiga tare da tarwatsa wani shirin kai babban hari ta hanyar luguden wuta daga sama.

Sojoji.
Dakarun rundunar sojojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @NigerianArmy
Source: Twitter

Sojoji sun dakile harin 'yan bindiga

Leadership ta rhoto cewa majiyoyin tsaro sun ce dakarun Sector 2 sun samu sahihan bayanan sirri kan shirin harin a yankin Kaura Namida, lamarin da ya sa suka yi gaggawar tura jami'ai tare da 'yan sa-kai na yankin domin dakile harin.

Kara karanta wannan

Mutanen da 'yan bindiga suka sace a wurin Ibada sun dawo gida, mutum 1 ya mutu a Ekiti

A yayin artabun da aka yi tsakanin bangarorin biyu, sojojin sun tilasta wa 'yan bindigar tserewa bayan sun yi musu mummunar ɓarna tare da jikkata da dama daga cikinsu.

An kashe kwamandan yan bindiga

A wani samame da aka kai a yankin Dogon Kade, sojojin da suka garzaya bayan samun rahoton harin da aka kai wa manoma sun kashe Alhaji Tukur, wanda aka bayyana a matsayin fitaccen kwamandan 'yan bindiga.

Haka zalika, bayanai sun nuna cewa Alhaji Tukur ƙani ne ga shugaban dabar 'yan bindiga da ake nema ruwa a jallo, Alhaji Shehu Bagiwaye.

Sauran 'yan bindigar da suka samu raunukan harbin bindiga sun tsere zuwa cikin dazukan da ke kusa, kamar yadda Daily Post ta kawo.

Haka kuma, a Sabon Gari da ke karamar hukumar Kaura Namoda, sojoji sun yi gaggawar isa yankin bayan samun rahoton motsin 'yan bindiga.

Da isowar dakarun, 'yan bindigar sun tsere zuwa cikin daji, inda binciken da aka yi ya kai ga kashe daya daga cikinsu tare da kwato wani babur da ake zargin suna amfani da shi wajen kai hare-hare.

Kara karanta wannan

"Ba zai yiwu ba," Hare haren 'yan bindiga sun kai mutane maƙura a jihar Sakkwato

Jirgin NAF.
Jirgin rundunar sojojin sama ta Najeriya yana kam hanyar zuwa aiki Hoto: @NigAirForce
Source: Twitter

Sojojin sama sun ragargaji 'yan bindiga 300

A wani gagarumin farmaki, Rundunar Sojin Sama da ke karkashin Operation Fansan Yamma ta farmaki 'yan bindiga kimanin 300 da ke tafiya a kan babura daga yankin Sunke-Kumbo zuwa yankin kogin Bayazaki.

Bayan samun bayanan sirri, Rundunar Sojin Sama ta tura jiragen yaki uku domin kai farmaki kan tawagar.

Lokacin da 'yan bindigar suka yi kokarin watsewa tare da fakewa karkashin bishiyoyi, jiragen yakin suka yi luguden wuta daidai kan inda suke, lamarin da ya jawo asarar rayuka masu yawa tare da dakile shirin harin.

Sojoji sun yi gumurzu da 'yan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile wani yunkurin yan bindiga na kai hari sansanin soji a Zamfara.

An ruwaito cewa sakamakon yadda sojojin suka yi fito-na-fito da maharan, 'yan ta'addan sun gaza cimma manufarsu, inda suka tsere daga yankin bayan sun yi watsi da harin.

Majiyoyi sun ce dakarun sun kuma kara tsaurara sintiri da sa ido a yankunan da ke kewaye domin hana 'yan ta'addan sake haduwa ko kuma kaddamar da wani sabon hari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262