Yadda Yan Ta'adda Suka Hallaka 'Yan Najeriya sama da 80,000 daga 2020 zuwa 2025
- Wani rahoton da cibiyar ORFA ta fitar ya bankado yadda 'yan ta'adda suka ci karensu babu babbaka a sassa daban-daban na Najeriya daha shekarar 2020 da 2025
- Daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su a wannan lokaci, an kashe mutane akalla 79,323 daga sassa daban-daban na Najeriya a 'dan lokacin
- Sai dai rahoton ya dora alhakin kisan a kan wasu kungiyoyi da suka hada da 'yan ta'addan Boko Haram da ISWAP, amma ba su kadai ba ne suka yi aika-aikar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Najeriya – Wani sabon rahoto na bincike na tsawon shekara shida da Observatory for Religious Freedom in Africa (ORFA) ta fitar ya bayyana cewa an kashe mutane 79,323 sakamakon hare-haren ta'addanci a Najeriya tsakanin shekarar 2020 zuwa 2025.
An ƙaddamar da rahoton ne a ranar Talata a birnin Jos, wanda ya ce ana kai akalla hare-hare bakwai a kowace rana, yayin da ake kashe kusan mutum 36 a kullum.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa rahoton ya ce daga cikin mutanen da aka kashe, 42,033 fararen hula ne, yayin da 37,290 suka kasance jami'an tsaro da kuma 'yan ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.
Harin yan ta'adda na jikkata yan Najeriya
A ruwayar da jaridar The Sun Nigeria ta kawo, kungiyar ta ce ta kwashe shekaru tana tantance bayanai daga wurare daban-daban domin gano yadda hare-haren ke faruwa da kuma masu aikata su.
A cewar ORFA:
"An kashe mutane 79,323 a Najeriya tsakanin 2020 da 2025, wanda ya yi daidai da hare-hare bakwai a kowace rana. Fiye da mutum 42,000 daga cikinsu fararen hula ne marasa laifi."
Binciken ya ƙalubalanci fahimtar da aka saba yi cewa Boko Haram da ISWAP ne suka fi haddasa tashe-tashen hankula a Najeriya.
A cewar rahoton, Boko Haram ta haddasa 8%na kashe-kashen fararen hula, yayin da ISWAP ta haddasa 4%, wanda gaba ɗaya ya zama kashi 12 cikin ɗari.

Kara karanta wannan
NDC ta ɗauki mataki bayan hukuncin kotu, ta fara tura sunayen 'yan takara ga INEC
An sako 'kungiyoyin Fulani' a ta'addanci a Najeriya
Sai dai ORFA ta yi ikirarin cewa ƙungiyoyin da ta kira 'kungiyoyin Fulani 'yan ta'adda' ne suka haddasa 44% na dukkannin mutuwar fararen hula, inda ta danganta musu kashe mutane 18,577, idan aka kwatanta da mutum 4,941 da ta ce Boko Haram da ISWAP suka kashe tare.s

Source: Getty Images
Sai dai ƙungiyar ta jaddada cewa tana bambance waɗannan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da al'ummar Fulani gaba ɗaya, ba a taru an zama daya ba.
Rahoton ya ce:
"ORFA tana taka-tsantsan wajen bambance ƙungiyoyin ta'addancin Fulani masu ɗauke da makamai da al'ummar Fulani baki ɗaya, domin mafi yawansu ba sa da hannu a tashin hankali."
Rahoton ya kuma yi ikirarin cewa an kashe Kiristoci 28,551 da Musulmi 13,224, sannan an yi garkuwa da Kiristoci 15,932 da Musulmi 15,272 a lokacin binciken.
ORFA ta ce bayananta sun samo asali ne daga binciken fili, abokan hulɗa na cikin gida, cibiyoyin ilimi, rahotannin kafafen yaɗa labarai da ƙungiyoyi masu zaman kansu, da kuma sahihan bayanan da aka tantance daga shafukan sada zumunta.
'Yan ta'addan ISWAP sun yi basaja
A baya, mun kawo labarin cewa 'yan ta'addan kungiyar ISWAP sun kutsa wata makarantar sakandare a Borno inda suka sace daliban da ke rubuta jarabawar NECO, lamarin da ya jawo gagarumin tashin hankali a yankin.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Borno. Nahum Daso, ya bada bayanai kan yadda 'yan ta'addan suka sace daliban Nahum Daso ya bayyana cewa 'yan ta'addan sun badda kama ne a lokacin da ake cin kasuwar garin.
A cewarsa, kodayake dakarun sojoji sun samu nasarar ceto mutane 10 daga cikin waɗanda aka sace, wasu daga cikin ɗaliban har yanzu ba a gano inda suke ba, sai dai ana ci gaba da aiki tukuru domin a ceto su.
Asali: Legit.ng

