Sheikh Ibrahim Khalil Ya Fadi Sirrin Gazawar Ronaldo a Kofin Duniya
- Shugaban majalisar malaman Kano kuma dan siyasa, Sheikh Ibrahim Khalil ya yi bayani game da shan kayen Cristiano Ronaldo a kofin duniya
- A sharhin da ya yi, malamin ya bayyana wasu abubuwa da ya ce su ne suka hana Ronaldo yin abin kirki a gasar duk da shi kwararre ne
- Ya yi magana ne a cikin jerin shirye-shiryen da ya ke gabatarwa karkashin shirin Mahangar Malam, yayin da ya ke bayani kan amfanin hadin kai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Fitaccen malamin addinin Musulunci kuma mai neman takarar gwamnan Kano a jam'iyyar ADC, Sheikh Ibrahim Khalil ya yi sharhi kan abin da ya shafi kwallo.
Malamin ya yi magana ne kan yadda fitaccen dan kwallo, Cristiano Ronaldo ya gaza tabuka abin a zo a gani a gasar cin kofin duniya ta 2026 da ake a Amurka.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro maganganun da Sheikh Ibrahim Khalil ya yi a kan Ronaldo ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Nasara na bukatar hada kai
Yayin bayani kan muhimmancin hadin kai, Sheikh Khalil ya ce mai yiwuwa da Ronaldo ya samu goyon bayan 'yan uwansa da ya taka rawa sosai a gasar cin kofin duniya.
Ya bayyana cewa duk himmar Ronaldo da kwazon shi, bai kai ga inda ya ke so ba a gasar sabada rashin mataimakan da suka dace.
Saboda haka ya bayyana cewa duk gogewar mutum, basirar shi da kwarewar shi, idan bai samu abokan aiki jarirtattu ba, ba zai kai ga gaci ba.
Ya ce:
"Duk kwarewar ka, ba za ka iya kawo nasara ba sai kana da abokan aiki."
Ya kara da cewa kamar yadda Hausawa suke cewa bishiya daya ba ta daji, yana da kyau mutum ya fahimci cewa shi kadai ba zai iya samun nasara a rayuwa ba.

Source: Getty Images
Bayani kan nasara a rayuwa
Bayan sharhin da ya yi, Sheikh Ibrahim Khalil ya kara da cewa duk wani abu da mutum zai nema a duniya, nasarar shi na da alaka da wadanda zai yi aiki da su.
Ya bayyana cewa nasarar mai mulki na da alaka ne da wandanda za a yi mulkin da su, domin suna taka muhimmiyar rawa a abubuwan da zai yi.
Malamin ya bayyana cewa babban darasin da jama'a za su koya a abin da ke faruwa da Ronaldo shi ne aiki tare da mutane masu nagarta ko da kadan ne.
'Duniya makaranta' Sheikh Khalil
Yayin da ya yi karin bayani kan dalilin sharhi kan kwallon kafa, malamin ya bayyana cewa duniya gaba dayan ta makaranta ce.
Saboda haka ya ce duk abin da mutum ya lura zai ga abin da zai dauka na darasi domin inganta rayuwarsa ta yau da kullum.
Rahoton ESPN ya nuna cewa kasar Spain ce tare cire Portugal da ci 1-0 a yayin da suka kara da juna a gasar cin kofin duniya ta 2026.
Cristiano Ronaldo ya furta bismillahi
A wani labarin, mun kawo muku cewa wani rahoto ya yi hasashen cewa dan wasan kasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya furta bismillahi a filin wasa.
An bayyana cewa ya furta bismillah ne a lokacin da ya zo bugun daga kai sai mai tsaron gida kuma ya samu nasarar zura kwallo a raga.
A shekarun baya, an jiwo Ronaldo na furta kalmomin da suke da alaka da Musulunci kamar 'Ma shaa Allah' da sauransu bayan zuwansa Saudi.
Asali: Legit.ng


