Hasken Musulunci: Ronaldo Ya Yi Nasara a Kofin Duniya bayan Furta Bismillahi

Hasken Musulunci: Ronaldo Ya Yi Nasara a Kofin Duniya bayan Furta Bismillahi

  • Wani bidiyo ya bazu a kafafen sada zumunta bayan an ga Cristiano Ronaldo yana furta kalmar "Bismillah" kafin ya zura kwallo a bugun fenariti
  • Masu sharhi a kafafen sada zumunta sun yi ikirarin cewa Ronaldo ya maimaita kalmar sau biyu kafin ya buga ƙwallon da ya zura a ragar Croatia
  • Tun bayan komawarsa ƙungiyar Al Nassr ta Saudiyya a 2023, Ronaldo ya saba amfani da kalmomin Larabci kamar "Assalamu alaikum" da sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - An ɗauki wani ɗan gajeren bidiyo a matsayin ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi jan hankali a gasar cin kofin duniya ta 2026.

Yayin da Cristiano Ronaldo ke shirin bugun fenariti a wasan zagaye na 32 tsakanin Portugal da Croatia, kyamarorin watsa shirye-shirye sun ɗauke shi kamar yana furta wasu kalmomi a hankali.

Kara karanta wannan

An cafke sarakuna 2 da matansu kan zargin alaka da yan ta'adda? gaskiya ta fito

Cristiano Ronaldo a filin wasa
Lokacin da Cristiano Ronaldo ya zurawaCroatia kwallo. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ronaldo ya fusta Bismillahi

Rahoton Al-Jazeera ya nuna cewa Ronaldo ya ce "Bismillah", yayin buga kwallo, wato kalmar Larabci mai nufin "Da sunan Allah."

Bidiyon ya bazu cikin sauri a kafafen sada zumunta

Wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa Ronaldo ya maimaita kalmar, wadda Musulmi ke furtawa kafin fara wani muhimmin aiki, sau biyu kafin ya buga ƙwallon.

Yadda Ronaldo ya fafata a wasan

Abin da aka tabbatar shi ne cewa wasan ya gudana ne a birnin Toronto, inda Croatia ta fara cin ƙwallo ta hannun Ivan Perišić kafin Portugal ta samu fenariti.

Ronaldo mai shekara 41 ya zura ƙwallon cikin natsuwa, inda ya rama wa Portugal, wanda kuma ita ce ƙwallonsa ta farko a zagaye na 32 sannan ta uku a gasar baki ɗaya.

Daga baya Gonçalo Ramos ya ci ƙwallo bayan ƙarin lokaci, wanda ya bai wa Portugal nasarar 2-1 da kuma tikitin zuwa zagaye na gaba.

Kara karanta wannan

Zafi ya shiga Turai yana ta kashe mutane a Faransa da sauran kasashe

A daƙiƙun da suka gabaci bugun fenaritin ne aka ɗauki bidiyon da ya nuna kamar Ronaldo na motsa leɓunansa cikin abin da ya jawo ce-ce-ku-ce.

Cristiano Ronaldo ya zura kwallo a ragar Croatia
Lokacin da Ronaldo ya buga fenareti ayan furta Bismillahi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ma'anar kalmar Bismillahi

Kalmar "Bismillah" ta samo asali ne daga jimlar "Bismillahir Rahmanir Rahim", ma'ana "Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinƙai." Ita ce ke buɗe kusan dukkan surorin Alƙur'ani.

Malam Usman Al-Juzuri ya bayyana cewa Musulmi kan furta wannan kalma kafin cin abinci, fara aiki ko wani aikin halal da ke buƙatar natsuwa.

Ya ce:

"Kalmar ba wata addu'ar neman sa'a ba ce, domin a addinin Musulunci ana ɗaukar komai yana hannun Allah ne. Maimakon haka, furta ta wata hanya ce ta tuna Allah da kuma fara aiki da sunansa."

Ko da kuwa Ronaldo ya faɗi kalmar ko a'a, wasu sun ce irin wannan furuci zai dace da yanayin bugun fenariti da ke buƙatar cikakkiyar nutsuwa.

Ronaldo ya furta kalmomin Musulunci

Tun bayan komawarsa ƙungiyar Al Nassr ta Saudiyya a watan Janairu na 2023, Ronaldo ya ƙara nuna kusanci da al'adun Larabawa da Musulmi.

Shafin Muslim Network ya wallafa cewa a lokuta da dama ya kan gaishe da jama'a da "Assalamu alaikum", ya kuma yi amfani da kalmar "Shukran" ma'ana "Na gode."

Kara karanta wannan

Abdul Samad Rabiu BUA zai sayi kungiyar Kano Pillars? An ji gaskiyar zance

Haka kuma, lokacin da yake karɓar lambar yabo ta Globe Soccer Awards a ƙarshen shekarar 2025, ya ce idan Allah Ya so ("Insha Allah") zai kai ƙwallaye 1,000 a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa.

Ga bidiyon Ronaldo da shafin Globe Observer ya wallafa a X:

Ronaldo ya kafa tarihi a duniya

A wani labarin, mun kawo muku cewa Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi a duniyar kwallon kafa a gasar cin kofin duniya da ake.

Yayin da Ronaldo ya zura ƙwallo a gasar da ake yi a Amurka, ya zama ɗan kwallon na farko da ya sha kwallo a kofin duniya guda shida a jere.

Hakan na zuwa ne yayin da 'yan kwallo da dama a fadin duniya ke cigaba da fafatawa da nuna bajintar su a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 a Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng