Gaba da gabanta: Za'a gurfanar da Alkalin Alkalai a kotun CCT

Gaba da gabanta: Za'a gurfanar da Alkalin Alkalai a kotun CCT

Gwamnatin tarayya ta bukaci alkalin alkalan Najeriya, Walter Onnoghen, ya yi murabus daga kujerarsa bisa ga zargin mallakan makudan kudade da yaki bayyanawa gwamnati.

A kan yunkurin tilastashi murabus, gwamnatin tarayya zata gurfanar da Jastis Walter Onnoghen, ranan Litinin, 14 ga watan Junairu gaban kotun CCT dake karkashin jagorancin Jastis Danladi Umar dake Abuja.

Jaridar PRNigeria ta bayyana cewa ta ga takardar karan da kotu ta aikawa alkalin alkalan ranan Juma'a a gidansa dake Abuja. Ana zarginsa da kin bayyana wasu dukoyoyi da ya mallaka kuma hakan ya sabawa dokar kasa ga ma'aikacin gwamnati.

Bugu da kari, ana zarginsa da mallakan wata asusun kudi cike da kudaden wajen irinsu Dala, Fam, da Yuro. Shima ya sabawa dokar kasa musamman masu rike da kujerara iko.

Jastis Walter Onnoghen wanda shugaba Muhammadu Buhari ya nada da kyar bisa ga wasu zarge-zarge da ake masa na iya zama alkalin alkalai na farko a tarihin Najeriya da zai gurfana a gaban kotu.

KU KARANTA: Dakarun soji sun kama gungun batagari a Sokoto, hoto

Bola Tinubu, babban jigon jam'iyyar APC na kasa kuma babban shugaban kungiyar yakin zaben jam'iyyar APC, ya bayyana cewa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, ya juyawa jihar Legas baya a lokacin da aka tunkare shi kan wasu kudade da aka tauyewa jihar a fannin samar da wutar lantarki, lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Oluseun Obasanjo.

Tinubu ya sanar da hakan a lokacin da ya karbi bakuncin sarakunan gargajiya na al'umar Yarabawa a Abuja, a ranar Juma'a.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng