Hukumar gidajen yarin Najeriya
EFCC ta kai tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman, gidan yari na Kuje bayan kotu ta yanke masa hukuncin shekaru 75 kan laifuffukan rashawa.
Tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho, Dr Abdulrasheed Maina, ya faɗi a Abuja sakamakon raunin da ya samu. Ana ci gaba da ba shi kulawa a asibiti.
Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar Mazi Nnamdi Kanu ta sauya masa gidan yari daga Sokoto, tana mai cewa bukatar ba ta cika ka’ida ba.
A labarin nan, za a ji cewa babban fasto a Najeriya, Bishof Mathew Kukah ya bayyana cewa dalilansa na ganawa da Nnamdi Kanu a kurkuku a Sakkwato.
Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu ya roƙi kotu ta mayar da shi daga gidan yari na Sokoto zuwa yankin Abuja, yana cewa nisan wurin yana hana shi shirya daukaka kara.
Rahotanni sun nuna cewa an jibge jami'an tsaro a ciki da wajem gidan yarin Sakkwato bayan labari ya nuna an kai mada jagoran IPOB, Nnamdi Kanu jihar.
Hukumar DSS ta tura Nnamdi Kanu zuwa gidan gyaran hali na Sokoto bayan kotun tarayya ta Abuja ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai bisa laifin ta’addanci.
Wata tawaga da lauyoyi da Omoyele Sowore ya jagoranta ta ziyarci Sheikh Abduljabbar a gidan yarin Kuje, tana zargin shari’arsa na cike da tasirin siyasa.
Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta rage hukuncin wasu fursunoni 86 ciki har da Maryam Sanda saboda cancantarsu.
Hukumar gidajen yarin Najeriya
Samu kari