Ba zaka iya yi min adalci ba, ka cire kanka daga shari'a ta, Onnoghen ga shugaban kotun CCT

Ba zaka iya yi min adalci ba, ka cire kanka daga shari'a ta, Onnoghen ga shugaban kotun CCT

- Onnoghen ya bukaci chiyaman din kotun manyan laifuka da ya tsame hannuwan shi daga shari'ar shi

- A cewar Onnoghen, hukumar yaki da rashawa na zargin Umar da wasu laifuka

- Don haka bai kamata ace yana da hannu a shari'a ba

Limamin Coci zai dauki Almajirai ya koya musu sana'a, Limaman Musulmi sunce anqi wayon
Limamin Coci zai dauki Almajirai ya koya musu sana'a, Limaman Musulmi sunce anqi wayon
Asali: Twitter

Dakataccen alkalin alkalai, Walter Onnoghen a jiya yace wa chiyaman din kotun manyan laifuka, Danladi Umar da ya cire kanshi daga shari'ar shi akan bayyana kadarorin shi saboda akwai yuwuwar yaki yin adalci.

Mai shari'ar ya zargi shugaban da yanke mishi hukunci ba tare da jin shari'ar ba ko gurfanar dashi a gaban kotun manyan laifukan.

Onnoghen yace Umar mara gaskiya ne a boye tunda shima yana fuskantar zargi daga hukumar yaki da rashawa.

Ya fadi hakan ne sakamakon takardar dokokin masu shari'ar manyan laifuka da aka kara bitar su a 2016.

GA WANNAN: Bayan an gano gwamnonin Nijar a taron APC a Kano, Ribadu ya maida martani

Lauyoyin shi sun hada da Chris Uche (SAN), Chief Sebastine Hon(SAN), Okon Efut(SAN), Chief Ogwu Onoja (SAN), Noah Abdul da George Ibrahim.

Ta bakin lauyoyin shi yayi ikirarin cewa Umar ya rubuta kuma yasa hannu akan dokar umarnin "Duk wanda ke fuskantar shari'a ba tare da an yanke mishi hukunci ba, ya koma gefe har sai an gama shari'ar."

A ranar 25 ga watan Janairu 2019 shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Onnoghen kuma ya rantsar da mukaddashin alkalin alkalai Tanko Muhammad.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel