Babbar Kotu Ta Tura Tsohon Shugaban CCT Ta Najeriya Gidan Yari a Abuja
- Babbar Kotun Birnin Tarayya sbuja ta tura tsohon shugaban CCT na kasa, Danladi Umar gidan yarin Kuje bayan gurfanar da shi a gabant
- Gwamnatin tarayya ta tuhume shi da laifuffuka hudu da suka shafi rashawa, inda ake zarginsa da karbar sama da N13.9m ta asusun matarsa
- Kotu ta dage sauraron bukatar belin tsohon shugaban na CCT zuwa ranar 15 ga watan Yuli, 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria -Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke zamanta a Maitama ta ba da umarnin a tsare tsohon shugaban Kotun Da'a ta Kasa (CCT), Danladi Umar, a gidan yarin Kuje.
Mai shari'a Peter Kekemeke ne ya bayar da umarnin bayan gwamnatin tarayya ta hannun EFCC ta gurfanar da tsohon shugaban CCT kan tuhume-tuhume hudu da suka shafi rashawa.

Source: Getty Images
Dalilin gurfanar da tsohon shugaban CCT
A cewar gwamnatin tarayya, binciken da aka gudanar ya nuna cewa Danladi Umar ya yi anlmfani da mukaminsa wajen amfanar da kansa yayin da yake jagorantar CCT, kamar yadda jaridar Vanguard ta kawo.
Ana zarginsa da cewa a 2021 ya yi amfani da asusun bankin matarsa wajen karbar Naira miliyan 5.5 daga wani dan kwangilar da aka ba aikin fentin hedkwatar CCT da ke Abuja.
Haka kuma, gwamnati ta ce a ranar 25 ga Janairu, 2024, ya sake amfani da asusun matarsa wajen karbar Naira miliyan 6 daga wani dan kwangilar da ya gudanar da aikin hada bayanan CCT a na'ura.
Baya ga haka, ana zarginsa da umurtar wani dan kwangila ya biya Naira miliyan 2.43 kudin makarantar 'yarsa a Jami'ar Baze da ke Abuja.
Wadannan laifuffukan a cewar gwamnatin tarayya, suna karkashin sashe na 19 na Dokar ICPC ta shekarar 2000.
Kotu ta dage sauraron bukatar beli
Bayan an karanta masa tuhume-tuhumen, Danladi Umar ya musanta aikata ko ɗaya daga ciki nan take.
Lauyan gwamnati, Christopher Mshelia, ya bukaci kotu ta tsare shi a gidan gyaran hali tare da sanya ranar fara shari'ar.
Sai dai lauyoyin wanda ake kara sun roki kotu ta ba da belin tsohon shugaban CCT har sai an kammala shari'ar, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Source: Facebook
Masu gabatar da kara sun bayyana cewa sun karbi takardar neman belin ne a wannan rana, saboda haka suna bukatar lokaci domin mayar da martani.
Saboda haka, Mai shari'a Kekemeke ya dage sauraron bukatar belin zuwa ranar 15 ga watan Yuli, 2026, tare da umarnin a tsare Danladi Umar a gidan yarin Kuje.
Kotu ta shirya hukunci kan kadarorin Malami
A wani rahoton, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya ta ɗage yanke hukunci kan buƙatar hukumar EFCC ta kwace kadarorin tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami.
EFCC ta ce tana zargin kadarorin guda 57 an mallake su ne ta haramtacciyar hanya don haka akwai bukatar karbe su, a mika wa gwamnatin tarayya.
Sai dai lauyan Malami da sauran waɗanda ake ƙara, Adedayo Adedeji, ya buƙaci kotu da ta yi watsi da buƙatar EFCC tare da soke umarnin wucin gadi na kwace kadarorin da aka bayar a baya.
Asali: Legit.ng


