Ta’addanci: Kotu Ta Zauna Kan Shari’ar Shugaban Miyetti Allah kan Tuhume Tuhume
- Shugaban Miyetti Allah a Najeriya, Bello Bodejo, ya yi magana a kotu game da tuhume-tuhume 12 da EFCC ta shigar
- Hukumar EFCC ta gurfanar da Bodejo a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin da ya shafi dala miliyan 2.63
- Bayan karanta tuhume-tuhumen a kotu, Mai Shari'a Inyang Ekwo ya dage ci gaba da sauraron shari'ar domin ci gaba da gudanar da shari'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban kungiyar Miyetti Allah na kasa, Alhaji Bello Bodejo, ya gurfana a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Bodejo ya musanta dukkan tuhume-tuhume 12 da ake masa na zargin wanke kudade da daukar nauyin ta'addanci da suka shafi dala miliyan 2.63.

Source: Facebook
Zargin da ake yi wa Bello Bodejo
Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Ta'annati (EFCC) ce ta gurfanar da Bodejo a gaban Mai Shari'a Inyang Ekwo, tana zarginsa da aikata laifukan kudi da suka shafi wannan makudan kudade, cewar Leadership.
A farkon zaman kotun, lauya mai gabatar da kara na EFCC, Wahab Shittu (SAN), ya sanar da kotun cewa an tsara zaman ne domin wanda ake kara ya amsa tuhume-tuhumen da aka gabatar a kansa.
Lauyan mai kare Bodejo, Ahmed Raji (SAN), bai nuna wata adawa da ci gaba da shari'ar ba, lamarin da ya bai wa kotu damar karanta tuhume-tuhumen a bainar jama'a.

Source: Twitter
Martanin Bodejo kan zarge-zargen ta'addanci
Bayan an karanta tuhume-tuhume 12 da ake masa a gaban kotu, Bello Bodejo ya musanta dukkan zarge-zargen, yana mai bayyana cewa ba shi da laifi.
Takardun kotu sun nuna cewa an rubuta tuhume-tuhumen ne a ranar 24 ga Yuni, sannan aka shigar da su a kotu ranar 25 ga Yuni, inda aka bayyana Bello Bodejo a matsayin wanda ake kara shi kadai.
Masu gabatar da kara suna kokarin tabbatar da zargin wanke kudade da kuma daukar nauyin ta'addanci da ake yi wa shugaban kungiyar Miyetti Allah yayin da shari'ar ke ci gaba.
Bayan kammala zaman na ranar, Mai Shari'a Inyang Ekwo ya dage ci gaba da sauraron shari'ar zuwa wani lokaci domin ci gaba da gudanar da shari'ar.
Bayan Bello Bodejo ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa, shari'ar za ta wuce mataki na gaba na sauraron shari'ar laifi, cewar Sahara Reporters.
Ana sa ran masu gabatar da ƙara da masu kare wanda ake ƙara za su gabatar da hujjoji da bayanansu kafin kotu ta yanke hukunci kan zarge-zargen.
Bodejo: Miyetti Allah sun roki Tinubu
An ji cewa Fulani makiyaya sun roƙi shugaba Bola Tinubu da hukumomin Najeriya su sa baki domin a saki shugabansu, Alhaji Abdullahi Bello Bodejo.
Sun ce an taba kama Bello Bodejo sau uku tun daga shekarar 2024, inda suka ce a lokuta biyu da suka gabata an janye tuhuma a kansa.
Kungiyar Fulanin ta buƙaci a tabbatar an masa adalci, an bi doka da kare haƙƙin Bodejo kamar yadda ya kmata a yi wa kowane dan kasa.
Asali: Legit.ng

