Matakai 4 da za a Bi kafin Tabbatar da 'Yan Sandan Jihohi a Najeriya

Matakai 4 da za a Bi kafin Tabbatar da 'Yan Sandan Jihohi a Najeriya

Yayin da ake cigaba da magana kan kafa 'yan sandan jihohi a Najeriya, mun tattaro muku muhimman matakan da za a bi kafin tabbatar da su.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Majalisar tarayya ta amince da kafa 'yan sandan jihohi a Najeriya da niyyar samar da hanyar magance matsalolin tsaro.

Shugaban kasa Bola Ahmed Bola Tinubu, gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki sun nuna amincewa da kafa 'ya sandan jihohi.

'Yan sandan Najeriya a bakin aiki
Wasu jami'an 'yan sanda na fareti a Abuja. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu matakan da doka ta tanada da dole za a bi su kafin a amince da kafa dokar 'yan sandan.

1. Tura kudiri Majalisar tarayya

Mataki na farko da doka ta ce za a dauka domin tabbatar da an samar da 'yan sandan jihohi shi ne tura kudirin ga 'yan majalisar tayyara daga shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Yaki zai sauya: Gwamnan Sokoto ya raba motocin sulke ga sojoji, 'yan sanda

Vanguard ta wallafa cewa tun a baya shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar dokoki ta kasa da kudirin gyaran kundin tsarin mulki, inda yake neman kafa ‘yan sandan jihohi.

Kudirin ya nemi a gyara wasu tanade-tanaden kundin tsarin mulkin 1999 domin samar da tsarin doka da zai ba da damar kafa ‘yan sandan jihohi a duk faɗin tarayya.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a majalisar tarayya. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Hakan na zuwa ne bayan shugaban ƙasa ya sha yin kira da a yi gyaran kundin tsarin mulki domin bai wa jihohi damar taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaron yankunansu.

2. Amincewar Majalisar tarayya

Bayan shugaban kasa ya tura kudiri majalisar tarayya, 'yan majalisa za su yi nazari game da shi domin yarda ko kuma kin amincewa da shi.

Bayan tura bukatar shugaban kasar, Daily Trust ta rahoto cewa majalisar dattawa ta amince da kudirin domin gyara kundin tsarin mulkin 1999.

Da amincewar da aka yi da kudirin, zai maye gurbin tsarin rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yanzu da sabon tsari mai runduna biyu, wato rundunar ‘yan sandan tarayya da kuma rundunonin ‘yan sandan jihohi.

An yi nazari kan kudirin ne bayan Sanata Opeyemi Bamidele, ya gabatar da muhimman ƙa’idojinsa. Daga nan ne ya tsallake karatu na biyu, aka yi masa nazari sashe-sashe, sannan aka amince da shi a karatu na uku.

Kara karanta wannan

Duk da zargin badakala, Tinubu ya naɗa Gbajabiamila cikin kwamitin ƴan sandan jihohi

'Yan majalisar dattawa
Sanata Godswill Akpabio a majalisar dattawa. Hoto: Nigerian Senate
Source: Twitter

Amincewar ta biyo bayan cikakken nazari da aka yi wa kudirin sashe-sashe, inda sama da kashi biyu bisa uku na sanatoci suka kada kuri’ar goyon baya.

3. Tura kudirin zuwa jihohi

Bayan majalisar tarayya ta amince da kudirin, tura shi zuwa majalisun jihohi, wanda shi ne mataki na gaba domin samun amincewar su.

A yanzu, majalisar dokoki ta kasa ta aika kudirin kafa ‘yan sandan jihohi zuwa majalisun dokokin jihohi 36 a fadin kasar nan.

Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar dattawa, Yemi Adaramodu, ne ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da jaridar da jaridar Punch.

A cewarsa, majalisun dokokin jihohi da gwamnoni sun riga sun san da zuwan kudirin bayan shawarwarin da aka gudanar kafin majalisar dokoki ta Ƙasa ta amince da shi.

Gwamnonin jihohin Najeriya
Yadda gwamnonin Najeriya suka yi wani taro a Abuja. Hoto: Abdul No Shaking
Source: Facebook

4. Amincewar shugaban kasa

Idan jihohi suka amince da kudirin, za a maido shi wajen shugaban kasa ya rattaba hannu a kan shi, wanda hakan zai nuna ya zama doka.

Kara karanta wannan

Ma'aikatar bogi: Kujerun manyan jami'an Tinubu na rawa, ana kira a kore su

A halin yanzu, shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar da kwamitin domin tsara tsarin doka da za a bi wajen aiwatar da kafa ‘yan sandan jihohi a faɗin ƙasar.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Bola Tiubu yayin wani jawabi ga 'yan Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ne ya ƙaddamar da kwamitin a fadar shugaban kasa.

Matsayar gwamnonin Arewa

A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnonin jihohin Arewa 19 da sarakunan gargajiya sun gudanar da taro a kan tsaro a jihar Kaduna.

Shugaban gwamnonin Arewa, Muhammad Inuwa Yahaya ya bayyana cewa sun amince da samar da 'yan sandan jihohi a Najeriya.

Sun bayyana cewa suna da tabbaci kan cewa matakin zai taimaka wajen rage matsalar tsaro da ta addabi jihohin Arewa a baya-bayan nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng