Duniya Rumfar Kara: Basarake Ya Rasu a Bauchi Kwana 6 da Naɗa Shi Sarauta

Duniya Rumfar Kara: Basarake Ya Rasu a Bauchi Kwana 6 da Naɗa Shi Sarauta

  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa basarake ya riga mu gidan gaskiya kwanaki bayan nada shi sarauta a jihar Bauchi
  • An tabbatar da rasuwar Sarkin Gorondo, Alhaji Lamaran Muhammad Gidado, bayan ɗan gajeren rashin lafiya
  • Marigayin ya kasance Marafan Alkaleri, kuma an naɗa shi Sarkin Gorondo kwanaki shida kacal kafin rasuwarsa da ta faru a ranar Talata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gorondo, Bauchi - Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi jana'izar wani basarake da ya riga mu gidan gaskiya a jihar Bauchi.

An tabbatar da rasuwar marigayin, Alhaji Lamaran Muhammad Gidado, Marafan Alkaleri kuma Sarkin Gorondo, bayan ya yi fama da ɗan gajeren rashin lafiya.

An rashin wani basarake a Bauchi
Marigayi Sarkin Gorondo a jihar Bauchi, Alhaji Lamaran Muhammad Gidado. Hoto: Labari daga Bauchi.
Source: Facebook

Wasu majiyoyi daga Zamani TV sun ce mutuwar marigayin ta girgiza iyalansa, al'ummar Gorondo da daukacin Masarautar Bauchi.

Kara karanta wannan

An tafka babban rashi: Daya daga cikin manyan limaman masallaci ya rasu a Kwara

Sarki ya rasu bayan nada shi sarauta

Marigayin ya rasu ne a ranar Talata, 21 ga watan Yulin 2026, bayan kwanaki shida kacal da aka naɗa shi a matsayin Sarkin Gorondo.

Mutuwar basaraken ta zo ba zato ga jama'ar da ke sa ran zai jagorance su a jihar bayan nada shi mukami.

An bayyana cewa an yi sallar jana'izarsa da misalin ƙarfe 10:00 na safiyar ranar Laraba 22 ga watan Yulin 2026.

An tabbatar da cewa an yi sallar jana'izar a Kofar Mai Martaba Sarkin Bauchi, Dakta Rilwanu Suleimanu Adamu.

Iyalan marigayin, masarauta da al'ummar Gorondo sun karɓi wannan babban rashi cikin alhini.

Ana ci gaba da bayyana jimami tare da yi masa addu'o'in neman gafara duba da irin gudunmawar da ya ba al'umma.

Sarkin Gorondo ya rasa ransa a Bauchi
Taswirar jihar Bauchi da aka yi rashin basarake. Hoto: Bauchi.
Source: Original

Masu alhini sun yi ruwan addu'o'i ga marigayin

Masu alhini sun roƙi Allah Madaukakin Sarki Ya jiƙan Alhaji Lamaran Muhammad Gidado da rahama. Sun kuma nemi Allah Ya gafarta masa dukkan kura-kuransa.

Kara karanta wannan

Mai shekara 60 ya rasu bayan zuwa otel da budurwa, an samu maganin jima'i

Haka kuma, an yi addu'ar Allah Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. An kuma roƙi Ubangiji Ya ba iyalansa da masoyansa juriyar wannan babban rashi.

Al'ummar Gorondo da Masarautar Bauchi sun bayyana cewa za su ci gaba da tuna gudunmawar da marigayin ya bayar. Sun ce rasuwarsa babban gibi ne ga masarautar.

Haka kuma, an yi addu'ar Allah Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. An kuma roƙi Ubangiji Ya ba iyalansa da masoyansa juriyar wannan babban rashi.

Al'ummar Gorondo da Masarautar Bauchi sun bayyana cewa za su ci gaba da tuna gudunmawar da marigayin ya bayar. Sun ce rasuwarsa babban gibi ne ga masarautar.

Basarake ya rasu bayan dawowa daga Idi

A baya, mun ba ku labarin cewa an shiga wani irin yanayi bayan samun labarin rasuwar babban basarake a jihar Lagos, Oba Kabiru Agbabiaka.

Marigayin da ke sarautar Isolo a jihar ya rasu ne a yau Laraba 10 ga watan Afrilu bayan ya dawo daga sallar idi.

Shugaban karamar hukumar Isolo a jihar Lagos, Olasoju Adebayo shi ya tabbatar rasuwar basaraken inda ya ce an birne shi a ranar da yammaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.