Yaki zai Sauya: Gwamnan Sokoto Ya Raba Motocin Sulke ga Sojoji, 'Yan Sanda
- Gwamnatin jihar Sokoto ta raba motocin sulke 62 da kayan aikin tsaro na sama da Naira biliyan 27 ga hukumomin tsaro a jihar
- Gwamna Ahmad Aliyu ya ce an yi haka ne a karkashin shirin Operation Fight Terrorism da nufin magance ta'addancin 'yan bindiga
- Ministan tsaro Christopher Musa ya halarci bikin, ya kuma yi kira ga sojoji da 'yan sanda su kasance a fadake wajen yakar 'yan bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ta yi rabon motoci yaki 62 tare da kayan aikin tsaro daban-daban ga jami'an tsaro da ke aiki a jihar, a wani mataki da aka ce ya ci Naira biliyan 27.
Motocin, wadanda suka hada da motocin sulke na APC da babur, za a kai su ga rundunonin tsaro daban-daban domin karfafa yaki da barazanar tsaro a jihar.

Source: Facebook
Gwamna Ahmad Aliyu ya wallafa a Facebook cewa an kaddamar da motocin ne a karkashin shirin gwamnatin jihar da ake kira Operation Fight Terrorism.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta sassauta ba wajen inganta harkar tsaro da kuma kula da rayuwar jami'an tsaro.
Gwamna ya kara da cewa hukumar ta kafa wata rundunar tsaro ta 'yan sa-kai, kuma ta ba da motoci tsaro 40 domin ta taimaka wa hukumomin tsaron.
An kafa sansanin 'yan sanda
Gwamna Aliyu ya kuma sanar da kafa sansanin 'yan sanda a kauyen Tarah da ke cikin karamar hukumar Sabon Birni, domin wayar da kai kan rashin tsaro da ke addabar Gabashin jihar.
Bayan haka, ya bayyana cewa gwamnati ta gina gidaje biyar biyar ga dukkan rundunoni guda hudu, wato rundunar 'yan sanda ta Najeriya, sojin kasa, sojan sama, da NSCDC, a matsayin wani bangare na inganta rayuwar sojoji da 'yan sanda.
Gwamna ya kuma yabi Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda goyon bayan da yake bayarwa ga hukumomin tsaro wajen yaki da 'yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma.
Ministan tsaro ya yi gargadi
Christopher Musa, wanda ya halarci bikin, ya ce ɗaya daga cikin manyan matsalolin da rundunonin tsaro suke fuskanta shi ne rashin isasshen hanyar tafiya, musamman a yankuna masu duwatsu da jejin da 'yan bindiga ke amfani da su.
Ya yi imanin cewa samar da motocin zai taimaka wajen karfafa rundunonin tsaro sosai, kuma za su iya magance barazanar tsaro a Sokoto.
Janar Musa ya yi kira ga dukkan jami'an da za a tura tare da motocin, da su kasance masu mayar da hankali kuma su ɗauki mataki mai ƙarfi duk lokacin da suka fuskanci 'yan bindiga a lokacin aikin nasu.

Source: Facebook
Ya kuma jaddada cewa nasara ta dindindin a yaki da rashin tsaro na bukatar hadin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya, gwamnatocin jihohi, hukumomin tsaro da al'ummomin baki daya.
Kiran Sultan kan rashin tsaro
A wani labarin, Legit Hausa ta kawo muku cewa mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi kira a hada kai a Arewacin Najeriya wajen yaki da 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan
Duk da zargin badakala, Tinubu ya naɗa Gbajabiamila cikin kwamitin ƴan sandan jihohi
Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya bayyana haka ne yayin taro na musamman da shugabannin Arewa suka gudanar a Kaduna.
Sultan ya yaba da matakin da gwamnonin Arewa 19 suka dauka na hada Naira biliyan 1 duk wata domin yaki da 'yan ta'adda a sassan yankin.
Asali: Legit.ng

