Duk da Zargin Badakala, Tinubu Ya Naɗa Gbajabiamila cikin Kwamitin Ƴan Sandan Jihohi

Duk da Zargin Badakala, Tinubu Ya Naɗa Gbajabiamila cikin Kwamitin Ƴan Sandan Jihohi

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da kwamitin aiki na shugaban kasa don shirya dokokin aiwatar da 'yan sandan jihohi a kasar bayan amincewar majalisa
  • Majalisar dattawa ta riga ta zartar da kudirin gyara kundin tsarin mulki da zai kafa rundunar 'yan sanda ta tarayya da ta jihohi kasar nan 36 don inganta tsaro
  • Daga cikin manyan da Tinubu ya sanya a cikin kwamitin har da shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa da yan adawa ke so a bincika zan zargin badakala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja - Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kaddamar da kwamitin Shugaban Kasa kan dokokin 'yan sandan Najeriya wanda zai shirya tsarin doka don aiwatar da 'yan sanda na jihohi a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Majalisa na neman taka wa Tinubu birki kan tubabbun yan ta'adda a Najeriya

An kaddamar da kwamitin a gidan gwamnatin tarayya a Abuja a ranar Talata, 7 ga watan Yuli, 2026 inda shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya wakilci Tinubu.

Tinubu ya sanya Gbajabiamila a kwamitin yan sandan jihohi
Femi Gbajabiamila tare da Bola Ahmed Tinubu Hoto: Aso Rock Villa
Source: Facebook

Channels TV ta wallafa cewa an kaddamar da wannan kwamiti bayan majalisar dattawa ta zartar da kudirin gyara kundin tsarin mulki wanda ke neman kafa tsarin 'yan sanda biyu, wato Rundunar 'Yan Sanda ta Tarayya da ta jihohi.

Tinubu ya magantu kan yan sandan jihohi

Jaridar Punch ta kawo labarin cewa Tinubu ya ce duk da cewa gyaran kundin tsarin mulki ya shimfida harsashin aiwatar da 'yan sanda na jihohi, kudirin dokokin 'yan sanda ta kasa shi ne zai bayar da cikakken tsari na aiwatar da shi.

Ya ce kudirin zai kafa ka'idoji na mafi karancin ma'aunin aikin 'yan sanda, sharudan shirye-shiryen jihohi, hadin gwiwar tarayya da jihohi, kiyaye hakkin dan Adam, da tsarin canja ma'aikata.

Shugaban ya kuma ce kwamitin zai samar da kudirin doka mai inganci kafin a kammala tsarin gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya.

A kalamansa:

"Ba za mu jira a kammala tsarin kundin tsarin mulki ba kafin mu fara wannan muhimmin aiki ba."

Kara karanta wannan

Yan sanda sun cafke mahaifin wanda ya kafa ma'aikatar bogi a gwamnatin Tinubu

Gbajabiamila zai jagioranci kwamiti

Gbajabiamila zai jagoranci kwamitin, wanda ya hada da Babban Lauyan Tarayya, Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, da Sufeton 'Yan Sanda.

Gbajabiamila ne zai jagoranci duba yadda za a tsara aikin yan sandan jihohi
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila Hoto: @femigbaja
Source: Twitter

Haka nan, shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya NBA da shugaban gwamnonin Najeriya NGF suna cikin kwamitin da zai duba tsarin 'yan sandan.

Babban Lauyan Tarayya Lateef Fagbemi ya ce ana yin wannan aiki a lokacin da ya dace domin kasar na fuskantar kalubalen tsaro.

Ya roki gwamnonin jihohi da su tabbatar da cewa majalisun jihohinsu sun amince da gyaran kundin tsarin mulki da sauri domin dokar ta fara aiki gadan-gadan.

Gbajabiamila: Atiku ya aika sako ga Tinubu

A baya, mun wallafa cewa dan takarar shugaban kasa a ADC, Atiku Abubakar ya nuna damuwa game da karuwar cin hanci da rashawa a Najeriya, wanda ya ke ganin yana karuwa a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Atiku Abubakar ya bukaci Shugaba Tinubu ya dakatar da Femi Gbajabiamila tare da binciken zargin karɓar Naira miliyan 400 da ake yi masa da kuma zargin yana da masanaiya a kan hukumar bogi da aka samar.

Sai dai Femi Gbajabiamila ya musanta sanin PFIPC ko naɗa Adeniyi Adeyemi a matsayin shugabanta, yayin da Adeyemi ke zarginsa da neman kaso daga kuɗin fara aikin hukumar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng