Sakataren APC da Ya Je Kara a Kotu Ya Dawo Zai Biya Tarar Naira Miliyan 100

Sakataren APC da Ya Je Kara a Kotu Ya Dawo Zai Biya Tarar Naira Miliyan 100

  • Nkemakolam Ukandu ya tuhumi wasu alkalan kotun tarayya da son rai sakamakon shari’ar David Mark da Nafiu Bala
  • Sakataren walwalan na ADC ya yi karar alkalan; John Tsoho da Peter Lifu, yana zarginsu da son kai wajen shari’a
  • Ukandu bai yi nasara a kotu ba, sai dai ma alkali ya umarce shi ya biya N50m ga duka alkalan da ya jefa da zargi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Babban kotun tarayya mai zama a garin Abuja ta yi fatali da karar da Nkemakolam Ukandu ya shigar a kan wasu manyan alkalanta.

Nkemakolam Ukandu ya yi karar Babban alkalin kotun tarayyar, John Tsoho da kuma Peter Lifu, yana zarginsu da nuna son kai a shari’a.

Shugaban ADC
Shugaban ADC na kasa David Mark tare da wasu manyan jam'iyya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An kai karar alkalai 2 zuwa kotun tarayya

Jaridar Punch ta ce a karshe an ci tarar Ukandu har N100m saboda rashin shigar da kara da kyau da kuma kin halartar zaman kotun da aka yi.

Kara karanta wannan

‘Dan takarar gwamna a PDP bai son tazarce ya ce wa’adi 1 rak ya ishe shi

Mista Ukandu shi ne Sakataren walwala na jam’iyyar ADC na kasa kuma kotu ta bukaci ya biya N50m ga kowane alkalin da ya jefa da zargi.

Alkali Salim Ibrahim ya yi hukunci wanda ya shigar da karar zai ba kowane daga cikin Mai shari’a Tsoho da Mai shari’a N50m nan da kwanaki 14.

"An kuma yi umarni wanda ya shigar da kara zai biya N50m ga kowane daga cikin wanda ake tuhuma na biyu da na uku, kwanaki 14 daga ranar hukuncin nan."

Sakataren ADC ya so NJC ta binciki alkalan

Ukandu ya yi karar Majalisar shari’a ta kasa, Alkali Tsoho da Alkali Lifu, yana so a tilasta wa NJC yin bincke a kan zargin da yake yi wa alkalan.

Sakataren jin dadin na ADC yana zargin wadannan alkalai na kotun tarayya da rashin gaskiya, cin amanar ofis da kuma son kai wajen yin shari’a.

An kai wannan kara ne sakamakon rigimar shari’ar da aka yi tsakanin Nafiu Bala Gombe da shugabancin ADC karkashin David Mark.

Da aka je sauraron karar a ranar Litinin, 6 ga watan Yuli 2026, an samu alkali John Tsoho da abokin aikinsa Peter Lifu J.U.K da J. U. K. Igwe (SAN).

Kara karanta wannan

Peter Obi ya burma matsala da aka bukaci ya biya N50bn

Lauya J. U. K. Igwe (SAN) wanda shi ma yana zaune a cikin kotun tarayyar ya fada wa alkali cewa an sanar da wadanda ake kara game da shari’ar.

Nan take lauyan wadanda ake kara ya roki kotu ta yi watsi da shari’ar mai lamba ABJ/CS/1165/2026 kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto.

Sakataren APC
Wasu shugabannin jam'iyyar ADC Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yadda lauya ya nemi Ukandu ya biya tara

Babban lauyan ya kuma tuna wa alkali cewa tun da wanda ya shigar da kara ya ki zuwa kotu, a dokar kasa yana damar da za a biya shi wasu kudi.

An kuma fada wa kotu cewa Ukandu ya canza adireshinsa yayin da ake shari’ar saboda kawai a gagara aika masa da takardar zaman kotun da za a yi.

Alkali Salim Ibrahim ya karbi bukatunsa, ya kori karar kuma ya yi umarni a biya N100m, yake cewa ba za ta yiwu a cigaba da tafiya a haka ba.

Ana shari'a da Godwin Emefiele a kotu

Godwin Emefiele ya jawo ana son cusa Marigayi Muhammadu Buhari a shari’ar satar $6m a CBN duk da ya mutu kimanin shekar guda da suka shude.

Kara karanta wannan

Emefiele: Shekara 1 da rasuwa an nemi a jefa Marigayi Buhari a shari'ar satar $6.2m

Wani kwararre da aka dauko domin yin bincike yana so duk da Muhammadu Buhari ya rasu, EFCC ta yi shari’a da shi a kotu saboda kudin da aka sace.

Labarin ya bayyana cewa Jom Obazee yana ganin tunda ana ba mutum lambar yabo bayan ya cika, babu laifi idan an yi shari'a da marigayin a kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng