Dama Ta Samu da Gwamna Inuwa Ya Nada Sababbin Kwamishinoni 23 a Gombe

Dama Ta Samu da Gwamna Inuwa Ya Nada Sababbin Kwamishinoni 23 a Gombe

  • Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya zabo mutanen da yake son nadawa mukaman kwamishinoni a gwamnatinsa
  • Inuwa Yahaya ya mika sunayen mutane 23 ga Majalisar Dokoki ta jihar Gombe domin tantance da amincewa su zama kwamishinoni
  • Idan majalisar ta amince da sunayen mutanen, za a ba su ma'aikatu daban-daban da za su jagoranta a jihar Gombe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Gombe - Gwamna Inuwa Yahaya ya tura jerin sunayen mutane 23 da aka zaɓa a matsayin kwamishinoni zuwa Majalisar Dokoki ta jihar Gombe.

Gwamna Inuwa ya mika sunayen domin tantancewa da kuma tabbatar da su, a wani mataki na sake kafa majalisar zartarwa ta jihar Gombe.

Gwamna Inuwa ya nada sababbin kwamishinoni
Gwamna Muhammadu Inuwa na jihar Gombe Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Ismaila Misilli, ya fitar ranar Talata, 30 ga watan Yunin 2026, wadda aka sanya a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Kwamishina a Adamawa ya rasu, Gwamna Fintiri ya yi ta'aziyya

Sunayen mutanen da aka mika ga majalisa

Sunayen na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa mai kwanan wata 29 ga watan Yuni, 2026, wadda aka aikawa shugaban Majalisar, Rt. Hon. Abubakar Mohammed Luggerewo.

Mutanen da aka zaɓa su ne Alhaji Abdulkadir Mohammed Waziri, Alhaji Sanusi Ahmed, Hajiya Aishatu Mohammed Bose Ahmed, Engr. Bala Adams, Micah Sunday Hamman, Mohammed Saidu Mohammed, L.D. Faruk (Esq.), Muhammad Gambo Magaji, Farfesa Aishatu Umaru Maigari.

Sauran sun hada da Zubairu M. Umar (Esq.), Adamu Dishi Kupto, Shehu Yerima Abdullahi, Ibrahim Shehu Turaki, Sani Ahmed Haruna (Esq.), Moses Kyari Bolda, Yusuf K. Jalingo, Dr. Usman Maijama’a Kallamu, Prof. Danladi Adamu Bojude.

Hakazalika, akwai Alhaji Salihu Baba Alkali, Dr. Bertha Danja, Dr. Habu Dahiru, Nasiru Muhammad Aliyu da kuma Yusuf Abdu Kwadon (Esq.).

An nemi majalisa ta amince da sunayen

Bisa ga sanarwar, Gwamna Inuwa ya nemi amincewar Majalisar ne ga waɗannan naɗe-naɗe domin ƙarfafa tsara manufofi da aiwatarwa na gwamnatinsa.

"Gwamna Inuwa Yahaya, CON, ya mikawa Majalisar Dokoki ta jihar Gombe jerin sunayen mutane 23 da aka zaɓa domin naɗawa a matsayin kwamishinoni da mambobin majalisar zartarwa ta jihar Gombe, yana neman amincewar majalisar dokoki daidai da tanadin kundin tsarin mulki na Jamhuriyar tarayyar Najeriya."

Kara karanta wannan

Dama ta samu: Gwamnan Sokoto ya yi sababbin nade nade a gwamnatinsa

- Ismaila Uba Misilli

Inuwa Yahaya ya nada sababbin kwamishinoni
Gwamna Inuwa Yahaya yana jawabi a wajen taro Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Twitter

Ana sa ran cewa Majalisar Dokoki za ta fara tantance mutanen da aka zaɓa a cikin kwanaki masu zuwa.

Bayan an tabbatar da su, gwamnan zai rantsar da su kuma a ba su ma'aikatu daban-daban a da za su kula da su a matsayin mambobin majalisar zartarwa ta jiha.

Gwamna Inuwa ya yi maganar rashin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya yi magana kan rashin tsaron da ake fama da ita musamman a Arewacin Najeriya.

Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa rashin tsaro ne ke zama babbar barazana ga zaman lafiya da ci gaban Arewacin Najeriya.

Hakazalika gwamnan ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya, malamai, matasa, ƙungiyoyin mata da ƙungiyoyin fararen hula su haɗa kai wajen inganta zaman lafiya

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng