Manyan Masu Ruwa da Tsaki a Gombe Sun Dauki Wanda Suke So Ya Zama Gwamna a 2027
- 'Dan takarar gwamnan jihar Gombe na jam'iyyar APC, Jamil isyaku Gwamna ya samu karin goyon baya gabanin babban zaben 2027
- Masu ruwa da tsaki a jihar Gombe sun ayyana cikakken goyon bayansu ga Jamil Gwamna a wani taro da suka gudanar a Abuja
- Gwamna ya bayyana farin cikinsa bisa wannan goyon baya da ya samu, inda ya ce ya kara masa kwarin gwiwar yi wa al'umma hidima
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gombe, Nigeria - Wasu fitattun masu ruwa da tsaki a jihar Gombe sun bayyana goyon bayansu ga 'dan takarar gwamna na jam'iyyar APC a zaben 2027, Dr. Jamil Isyaku Gwamna.
Sun bayyana wannan matsaya ne a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Abuja ranar Lahadi da ta gabata.

Source: Facebook
Leadership ta rahoto cewa mahalarta taron sun ce sun yanke wannan hukunci ne bisa abin da suka bayyana a matsayin nagartar shugabancinsa, hangen nesansa da kuma jajircewarsa wajen ci gaba da bunƙasa jihar Gombe.
Manyan 'yan Gombe sun halarci taron
Mai magana da yawun Jamil Gwamna, Ibrahim Sani Shawai, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa Mai Bai wa Mataimakin Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Musamman, Dr. Aliyu Modibbo Umar, ne ya jagoranci taron.
Ya ce taron ya haɗa da tsofaffin ministoci, manyan hafsoshin soja da suka yi ritaya, tsofaffin manyan sakatarori, tsofaffin jakadu, farfesoshi, shugabannin 'yan kasuwa da kuma ƙwararrun matasa 'yan asalin jihar Gombe.
Jamil Gwamna ya samu goyon baya
A cewar sanarwar, mahalarta taron sun cimma matsaya baki ɗaya kan wasu shawarwari domin ƙarfafa APC gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
Daga cikin matakan da suka amince da su akwai bayyana Dr. Jamil Isyaku Gwamna a matsayin wanda suka fi so ya zama gwamnan Gombe a zaben 2027 karkashin inuwar jam'iyyar APC.
Masu ruwa da tsakin Gombe sun kuma yanke shawarar ƙara wayar da kan al'umma a ƙananan hukumomi 11 na jihar da ƙarfafa rajistar masu zaɓe.

Source: Facebook
Jamil Gwamna ya yi martani
Da yake mayar da martani bayan samun wannan goyon baya, Jamil Isyaku Gwamna ya ce hakan wani sabonbkira ne gare shi domin ci gaba da yi wa al'umma hidima.
Ya ce:
"Wannan goyon bayan da kuka ba ni ya ƙara mana ƙwarin gwiwar ci gaba da kasancewa masu mayar da hankali, masu biyayya ga doka da kuma masu sanya bukatun jama'a a gaba.
"Tare za mu tabbatar da cewa ci gaban da ake samu ba wai zai ci gaba kaɗai ba, har ma zai kai ga kowace al'umma, kowane gida da kuma kowane ɗan ƙasa."
PDP ta caccaki gwamnatin jihar Gombe
A wani rahoton, kun ji cewa PDP ta zargi gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya da bayar da miliyoyin Naira da filaye akalla hudu ga wani mawaki daga jihar Kano.
PDP ta ce ya dace a karkata wannan kudi zuwa ilimi, lafiya, noma, matasa da sauran ayyukan ci gaban jama'a a sassa daban-daban na jihar Gombe.
Jam'iyyar adawar ta nuna cewa wannan mataki ya zo ne a lokacin da jihar Gombe ke fuskantar kalubalen ilimi, inda ta ce akwai yara 787,619 da ba sa zuwa makaranta.
Asali: Legit.ng

