Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa a Kogi, Sun Hallaka Mutane da Dama yayin Hari
- Wasu mahara da ba a san ko su waye ba sun kai hari Okele-Ejule a ƙaramar hukumar Ofu ta Kogi, inda ake fargabar sun kashe mutane
- Mazauna yankin sun bayar da bayanai mabambanta kan musabbabin harin, yayin da wasu ke zargin siyasa
- Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da gano gawarwaki uku masu harbin bindiga, ta ce ta fara bincike domin gano gaskiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kogi - Wasu mahara da ba a san ko su waye ba sun kashe aƙalla mutum bakwai a wani sabon hari da suka kai garin Okele-Ejule da ke ƙaramar hukumar Ofu a jihar Kogi.
Rahotanni sun ce maharan sun sanya kayan sojoji, sannan suka kutsa cikin garin, inda suka riƙa harbe-harbe ba tare da zaɓe ba, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.

Source: Original
Ana ci gaba da binciken waɗanda suka mutu
Mazauna yankin sun ce adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa, domin an sake gano wata gawa a cikin wani daji da ke kusa da garin, cewar Punch.
Har yanzu ba a tabbatar da musabbabin harin ba, yayin da mazauna yankin ke bayar da bayanai mabambanta kan abin da ya jawo kashe-kashen.
Wasu majiyoyi daga al'ummar yankin sun yi zargin cewa wasu daga cikin waɗanda aka kashe suna da tarihin aikata laifuffuka, yayin da wasu kuma ke ganin akwai alaƙar siyasa da harin.
Haka kuma, wasu mazauna yankin sun bayyana cewa lamarin ya yi kama da sauran hare-haren da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba ke kaiwa.
Wata majiya ta yi zargin cewa wasu daga cikin mutanen da aka kashe sun kasance cikin sa idon Hukumar Tsaro ta DSS bisa zargin hannu a satar mutane da sauran laifuffuka a Ejule da maƙwabtan yankuna.
Majiyar ta ƙara da cewa:
"Ana zargin waɗanda aka kashe ko dai masu garkuwa da mutane ne ko kuma masu ba su bayanai."

Source: Facebook
Martanin rundunar ƴan sandan Kogi
Rundunar 'yan sandan Kogi ta tabbatar da aukuwar lamarin, tana mai cewa jami'anta sun gano gawarwakin maza uku a cikin wani daji da ke kan titin Ochadamu zuwa Umomi a ƙaramar hukumar Ofu.
Mai magana da yawun rundunar, ASP Saliu Oyiza Afusat, ta ce:
"A ranar Asabar, 4 ga Yuli, 2026 da misalin ƙarfe 4:35 na yamma, an samu rahoton gano gawarwakin maza uku a cikin wani daji da ke kan titin Ochadamu–Umomi a ƙaramar hukumar Ofu."
Ta ce bayan samun rahoton, jami'an 'yan sanda ƙarƙashin jagorancin DPO na sashen Ofu sun garzaya wurin, inda suka kwashe gawarwakin da ke ɗauke da alamun harbin bindiga.
Ta bayyana cewa an kai gawarwakin zuwa ɗakin ajiyar gawa na Asibitin Grimard da ke Anyigba domin ajiya da gudanar da gwajin gano musabbabin mutuwa, yayin da aka fara matakan binciken kotun coroner, cewar TheCable.
Yan bindiga sun kai wa ɗalibai hari
An ji cewa yan bindiga sun kai hari makarantar sakandare da ke Iluke Bunu a jihar Kogi, suka kashe mutum uku ciki har da mataimakin shugaba.
Rahotanni sun ce maharan sun kuma sace dalibai uku da wasu mazauna yankin yayin harin da suka kai makarantar.
Rundunar 'yan sanda ta ce har yanzu ba a tabbatar da sace mutane da yawa ba, tana mai cewa an kashe dan bindiga daya.
Asali: Legit.ng


