Daga Taimako, Ƴan Bindiga Sun Bindige Tsohon Sojan Najeriya Kusa da Abuja

Daga Taimako, Ƴan Bindiga Sun Bindige Tsohon Sojan Najeriya Kusa da Abuja

  • Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari wata unguwa da ke kan iyakar Abuja da Nasarawa, inda suka sace wata mata da tsakar dare
  • Wani tsohon sojan Najeriya ya fito domin taimakawa lokacin harin, amma maharan sun harbe shi har ya mutu nan take
  • Rundunar ƴan sanda ta fara bincike, yayin da jami'an tsaro suka ƙara ƙaimi domin ceto matar da aka sace tare da kamo waɗanda suka kai harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lafia, Nasarawa - An kashe wani tsohon jami'in rundunar sojin Najeriya tare da sace wata mata a harin ƴan bindiga.

Majiyoyi suka ce tsohon sojan ya rasa ransa bayan wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari wata unguwa da ke iyakar Abuja da Nasarawa.

Kara karanta wannan

Yadda dannau ya danne 'yan bindiga a barci, wadanda suka sace suka gudu

An harbe tsohon soja a Nasarawa
Hafsan sojojin Najeriya, Laftanar Kanal Waidi Shaibu. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Twitter

Rahoton Zagazola Makama ya ce ƴan sanda sun ce lamarin ya faru da tsakar daren a gida mai lamba 038 da ke yankin PGC, kusa da Jikwoyi a Abuja.

Ƴan bindiga sun sace mata a Nasarawa

Rahotanni sun ce maharan sun kutsa cikin gidan Silas Orite mai shekara 46, inda suka sace matarsa, Bukola Oluwatoyin Silas mai shekara 40, suka tafi da ita zuwa wani wuri da ba a sani ba.

Majiyoyin sun ƙara da cewa babban jami'in tsaron al'umma, Master Warrant Officer Reuben Yelwa mai shekara 61, tsohon jami'in rundunar sojin Najeriya, ya yi ƙoƙarin kai ɗauki lokacin harin.

Sai dai maharan sun harbe Reuben Yelwa har ya mutu a wurin yayin da yake ƙoƙarin taimaka wa mazauna yankin da harin ya rutsa da su domin ganin ya ba da gudummawa.

Yan bindiga sun sace mata bayan harbe tsohon soja
Taswirar jihar Nasarawa da ƴan bindiga suka kai farmaki. Hoto: Legit.
Source: Original

Matakin da ƴan sanda suka dauka kan lamarin

Rundunar ƴan sanda ta kai ziyara wurin da abin ya faru, ta tattara hujjoji tare da fara bincike domin gano musabbabin harin da kuma waɗanda suka aikata laifin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tafka barna a Sokoto, sun kashe basarake, ɗansa da wasu mutane

Jami'an tsaro sun ƙara ƙaimi wajen gudanar da bincike domin ceto matar da aka sace cikin ƙoshin lafiya tare da kamo maharan da suka kai harin, cewar Daily Post.

Haka kuma, an ƙarfafa sintiri da mamaye yankin domin dakile sake aukuwar irin waɗannan ayyukan ta'addanci da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma.

Wata majiya ta ce:

"An ƙara kaimi daga jami'an tsaro wajen ceto matar da aka sace cikin ƙoshin lafiya tare da kamo waɗanda suka kai harin, yayin da aka ƙarfafa ayyukan mamaye yankin domin hana sake aikata laifuka."

Yadda ƴan bindiga suka sace tsohon soja

A wani labarin, kun ji cewa yan bindiga sun yi garkuwa da Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya da matarsa yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wani biki a Katsina.

Maharan sun bude wa motar da suke ciki wuta, inda direbansa ya tsira da raunin harbi yayin da aka tafi da ma’auratan cikin daji.

Harin ya zo ne kwanaki kadan bayan 'yan bindiga sun kashe mutane 16 a kauyen Kiliya da ke karamar hukumar Dutsinma ta Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.