Yawan Kujerun Sanatoci da APC, PDP Ke da Su a Majalisa bayan Zaben Cike Gurbi

Yawan Kujerun Sanatoci da APC, PDP Ke da Su a Majalisa bayan Zaben Cike Gurbi

  • Jam'iyyar APC ta ƙara rinjaye a Majalisar Dattawa bayan ta samu kujeru da dama a sakamakon zabe bayan zaɓukan cike gurbi
  • Duk da ficewar wasu jiga-jiganta saboda rikicin zaɓen fitar da gwani, APC ta ci gaba da ƙarfafa rinjayenta ta hanyar nasarori da sauya sheƙa
  • Yanzu duk kujeru 109 na Majalisar Dattawa sun cika, yayin da PDP, LP da sauran jam'iyyun adawa suka rasa yawan kujerunsu sosai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jam'iyyar APC mai mulki ta ƙara ƙarfafa rinjayenta a Majalisar Dattawa bayan yawan sanatocinta ya kai 88.

Hakan ya biyo bayan rantsar da sanatoci huɗu da suka yi nasara a zaɓukan cike gurbi da aka yi a fadin Najeriya.

Yawan sanatocin APC da sauran jam'iyyun jam'iyyu a majalisa
Shugaban sanatoci, Godswill Akpabio yana jagiorantar zaman majalisa a Abuja. Hoto: The Nigerian Senate.
Source: Facebook

Kujerun da APC ta lashe a zabukan

Binciken Punch ya nuna cewa duk da ficewar wasu jiga-jigan APC saboda rikicin zaɓen fitar da gwani, jam'iyyar har yanzu na da rinjaye a Majalisar Tarayya.

Kara karanta wannan

Lamuran siyasa 6 da ka iya tasiri a zaɓen Najeriya na shekarar 2027

APC ta lashe ƙarin kujerun sanatoci uku a zaɓukan cike gurbi da aka gudanar a watan Yuni a Ondo, Enugu da Nasarawa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya rantsar da sababbin sanatocin huɗu a ranar 24 ga Yuni.

Sababbin sanatocin sun haɗa da Ikeje Asogwa mai wakiltar Enugu ta Arewa, Dayo Faduyile mai wakiltar Ondo ta Kudu da Danladi Envulu-Anza mai wakiltar Nasarawa ta Arewa.

Da wannan ƙarin, yawan sanatocin APC ya tashi daga 85 zuwa 88, abin da ya ƙara rage yawan kujerun jam'iyyun adawa.

Wannan ci gaba ya zo ne bayan wasu 'yan takara da sanatoci sun fice daga APC suna zargin shugabancin jam'iyyar da rashin adalci da kakaba 'yan takara.

Daga cikin waɗanda suka fice akwai tsohon Sufeto Janar na 'Yan Sanda, Abubakar Adamu, bayan ya sha kaye a zaɓen fidda gwani na gwamnan Nasarawa.

Sanatocin Bauchi ta Kudu, Shehu Buba, da na Bauchi ta Arewa, Sama'ila Dahuwa, sun koma PRP bayan sun kasa samun tikitin APC.

Wani ɗan Majalisar Wakilai daga Kano shi ma ya bar APC ya koma jam'iyyar NDC saboda rashin gamsuwa da tsarin zaɓen fidda gwani.

Kara karanta wannan

Rigima ta taso a APC bayan sauya 'yan takara, 'yan jam'iyya sun fara tutsu

Duk da waɗannan sauya sheƙu, APC ta ci gaba da faɗaɗa rinjayenta ta hanyar samun sababbin mambobi da kuma nasarorin zaɓukan cike gurbi.

APC ta sake karfafa ikonta a majalisar dattawa
Sanatocin Najeriya yayin zaman majalisa a Abuja.Hoto: The Nigerian Senate.
Source: Facebook

Yawan sanatocin APC a 2023

Lokacin da aka ƙaddamar da Majalisar Dattawa ta 10 a shekarar 2023, APC na da kujeru 59 kacal, amma yanzu ta mallaki 88.

A gefe guda, yawan sanatocin PDP ya ragu daga 36 zuwa biyar, yayin da LP ta rage daga takwas zuwa sanata guda.

Jam'iyyar NNPP ta rasa kujerunta biyu na farko, yayin da SDP ta rasa wakilci gaba ɗaya a Majalisar Dattawa.

APGA ta ci gaba da riƙe kujerarta guda ɗaya, yayin da ADC ke da sanatoci tara duk da ba ta da ko guda lokacin ƙaddamar da Majalisar.

Sabuwar jam'iyyar NDC tana da sanata guda ɗaya, wato jagoranta Seriake Dickson mai wakiltar Bayelsa ta Yamma.

Bayan rantsar da sababbin sanatocin, yanzu dukkan kujeru 109 da kundin tsarin mulki ya tanada a Majalisar Dattawa sun cika.

An sauya sunayen yan takarar APC

Da farko, an ji cewa kwamitin zartarwa na jam'iyyar APC ya cire tsohon gwamnan jihar Benue, Gabriel Suswam, da wasu 'yan takara 25 bayan zaben fitar da gwani.

Kara karanta wannan

Ana batun 2027, gwamna Sule ya tono sirrrin APC kan nasarar da ta ke samu

Rahoto ya nuna cewa sauye-sauyen da jam'iyyar APC ta yi sun shafi 'yan takarar majalisar dattawa da na majalisar wakilai da dama.

A cikin wata takarda da ta fitar, APC ta ce sabon jerin sunayen da aka fitar ne za ta yi amfani da shi, kuma shi aka turawa hukumar INEC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.