Sakon da Tinubu Ya Aika Kaduna bayan Umarnin a Farauto 'Yan Bindiga

Sakon da Tinubu Ya Aika Kaduna bayan Umarnin a Farauto 'Yan Bindiga

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi tir da harin da 'yan bindiga suka kai ƙauyen Naridon na jihar Kaduna inda aka yi wa mazauna yankin kisan kiyashi
  • Akalla mutum 30 da suka hada da mata da kananan yara sun mutu, yayin da aka kona gidaje da dama a harin da aka kai Karamar Hukumar Kauru ta jihar Kaduna
  • Bola Tinubu ya ce gwamnati ba za ta bari masu tada zaune tsaye su rusa zaman lafiyar Kaduna ba, tare da yin alkawarin hukunta masu laifin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi Allah wadai da harin da aka kai kauyen Naridon da ke mazabar Kamaru a Karamar Hukumar Kauru ta jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun shiga Kaduna da dare, sun kashe rayuka 30 sun kona gidaje

Ya kuma bayar da umarni ga jami'an tsaron kasar da su gaggauta kamo wadanda suka kai harin tare da ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Tinubu ya aika sako ga mutanen Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna Uba Sani, Shugaban kasa Bola Tinubu Hoto: Uba Sani/Bayo Onanuga
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa harin da aka kai da safiyar ranar Litinin 27 ga watan Yuli, 2026 ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 30, ciki har da mata da kananan yara, sannan an kona gidaje da dama.

Tinubu ya fusata da harin Kaduna

Kafar Channels ta wallafa cewa mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar da wata sanarwa a Abuja, inda Tinubu ya bayyana harin a matsayin mummunan aiki na ta'addanci da aka kai kan fararen hula marasa kariya.

Shugaban ya ce:

"Na umarci rundunar soji, 'yan sanda da hukumomin leken asiri da su kara kaimi wajen gudanar da aiki a yankunan da abin ya shafa domin gaggauta kamo masu laifin, ceto wadanda aka sace da kuma dawo da zaman lafiya."

Ya kara da cewa duk masu kokarin rusa zaman lafiyar da aka samu a jihar Kaduna ba za su wuce hukuncin hukumomin kasar nan ba.

Kara karanta wannan

An goyi bayan harbe 'yan ta'adda da zarar an gan su ba tare da jiran izini ba

Tinubu ya jajanta wa iyalan mamatan

Shugaban kasar ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, gwamnatin jihar da daukacin al'ummar Kaduna.

Tinubu ya nemi a farauto wadanda suka yi kisa a Kaduna
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Haka kuma ya tabbatar wa gwamnatin jihar da al'ummomin da abin ya shafa cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da mara musu baya wajen yaki da matsalar tsaro.

Tinubu ya ce:

"Gwamnatinmu na da cikakken kuduri na karfafa tsarin tsaro, samar da kayan aiki ga jami'an tsaro da kuma murkushe kungiyoyin masu aikata laifuka da ke kokarin kawo cikas ga zaman lafiyar kasa."

Ya kuma bukaci mazauna yankunan da su rika bai wa jami'an tsaro sahihan bayanai domin saukaka daukar matakin gaggawa.

Gwamnati ta magantu kan kumfa a Kaduna

A baya, mun wallafa cewa hukumar NESREA ta fara bincike kan wani sinadari da ake zargin ya zube a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja bayan wani hatsarin mota wanda ya ja hankalin jama'a da ke wajen.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya yi wa sojoji albishir, Tinubu zai sanar da karin albashinsu

NESREA ta tattara samfurin kumfar, ƙasa da ruwan rafin da ke kusa domin gwaji a dakin bincike saboda gano me ya faru a wajen. Biyo bayan tattara bayanan, hukumar ta gargadi jama'a da su guji taɓa kumfar.

A yayin ziyarar, jami'an NESREA sun gana da shugaban 'yan sanda na yankin Jere, ACP Sani Zubairu, da kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta kasa (FRSC) na yankin, da kuma shugaban al'ummar yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng