Oluremi Ta Bayyana Taimakon da Sarkin Musulmi Ya ba Tinubu da Gwamnatinsa
- Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yabawa Sarkin Musulmin Najeriya Muhammadu Sa’ad Abubakar
- Sarkin Musulmi ya bukaci shugabanni su ci gaba da neman taimakon Allah kan matsalar masu aikata ta'addanci, tare da addu'ar su tuba su rungumi zaman lafiya
- Gwamnan Sokoto Ahmad Aliyu da Sarkin Musulmi sun yabawa shirin Renewed Hope Initiative, suna cewa ya amfani mata, matasa, yara da iyalai a fadin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta gode wa Sarkin Musulmi, Mai Alfarma Muhammadu Sa’ad Abubakar.
Oluremi ta yaba masa ne saboda ci gaba da goyon baya da shawarwarin da yake bai wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu tun farkon kafuwarta.

Source: Twitter
Ta bayyana haka ne yayin wata ziyara da ta kai fadar Sarkin Musulmi a Sokoto, inda ta ce ta zo domin nuna godiya da kuma girmama irin gudunmawar da Sarkin yake bayarwa, cewar Tribune.
Oluremi Tinubu ta yabawa Sarkin Musulmi
Sanata Oluremi Tinubu ta tuna da dadadden alakar da ke tsakanin iyalansu, tana mai cewa Sarkin Musulmi ya kasance yana jagorantar gwamnati ta hanyar ba da shawarwari masu amfani.
Ta kara da cewa wannan ziyara ta musamman wata dama ce ta bayyana godiya gare shi saboda irin goyon bayan da yake ci gaba da bai wa gwamnatin shugaban kasa.
Da yake jawabi, Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya ce wajibi ne shugabanni su ci gaba da neman taimakon Allah musamman dangane da masu aikata miyagun laifuka a kasar.
Ya yi addu'ar Allah ya shiryar da masu aikata ta'addanci da sauran miyagu domin su tuba, su daina aikata barna, su rungumi rayuwa mai bin doka da zaman lafiya.
Sarkin Musulmi ya koda Sanata Oluremi Tinubu
Sarkin Musulmin ya kuma yaba wa Uwargidan shugaban kasa kan ayyukan da take gudanarwa ta karkashin shirin Renewed Hope Initiative (RHI), yana cewa shirin ya taba rayuwar miliyoyin 'yan Najeriya.
Gwamnan Sokoto, Dakta Ahmad Aliyu, shi ma ya gode wa Sanata Oluremi Tinubu bisa ziyarar da ta kai Sarkin Musulmi, yana mai cewa shirin RHI ya kawo sauyi ga rayuwar mata, matasa, yara da iyalai a fadin kasar.
A karshen taron, Sarkin Musulmi ya gayyaci malamai su yi addu'o'i ga Najeriya, Shugaba Bola Tinubu, Uwargidan shugaban kasa, gwamnan Sokoto, kansa da kuma daukacin al'ummar jihar Sokoto, cewar Punch.
An kaddamar da Marshal 1,500 a Sokoto
An ji cewa Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu Sokoto, ya yaye rukuni na biyu na jami'an Sokoto Marshals guda 1,550 da aka ɗauko daga dukkan ƙananan hukumomi 23 na jihar.
Gwamnan ya ce shirin ba wai samar da aikin yi kawai ba ne, har ila yau wata muhimmiyar dabara ce ta ƙarfafa tsaron al'umma, kare rayuka da dukiyoyi a Sokoto.
Gwamna Biodun Oyebanji na Ekiti ya yaba da matakin gwamnatin Sokoto, yana mai cewa wani abin koyi ne da sauran jihohin Najeriya za su iya kwaikwaya.
Asali: Legit.ng

