'Yan Kasa Sun Shiga Tsaka Mai Wuya da Gwamnati Ta Rufe YouTube, WhatsApp a Rasha
- Hukumar Roskomnadzor ta cire YouTube daga tsarin DNS na Rasha, lamarin da ya hana masu amfani shiga dandalin kai tsaye sai dai idan sun yi amfani da VPN
- Masana sun ce matakin na nuna yadda gwamnatin Rasha ke ƙarfafa ikon ta kan intanet ta hanyar takaita dandalan da ba ta da cikakken iko a kansu
- Rahotanni sun nuna cewa WhatsApp ma ya ɓace daga tsarin DNS na gwamnati, yayin da ake ci gaba da matsin lamba kan Telegram da sauran kafafen sadarwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Rasha - Hukumar da ke kula da harkokin intanet ta Rasha, Roskomnadzor, ta cire adireshin youtube.com daga tsarin DNS nata, abin da ya sa masu amfani ba za su iya shiga dandalin kai tsaye ba sai idan sun yi amfani da VPN.
Rahotanni sun ce matakin ya sa na'urorin masu amfani ba sa iya gano adireshin IP na YouTube, wanda ke hana bude shafin ba tare da wata hanyar kauce wa takunkumin gwamnati ba.

Source: Getty Images
WhatsApp da Telegram sun shiga matsin lamba
Baya ga YouTube, an kuma ce adireshin WhatsApp ya bace daga tsarin DNS na Roskomnadzor, yayin da gwamnatin Rasha ke ci gaba da matsin lamba kan manhajar Telegram, in ji rahoton DW.
Masana harkokin intanet sun bayyana cewa wannan na nuna yadda hukumomin kasar ke kara takaita dandalan sadarwa da ba sa karkashin cikakken ikon gwamnati.
Yadda tsarin DNS da VPN ke aiki
Masana sun bayyana cewa DNS na aiki ne kamar kundin adireshin intanet da ke hada sunayen shafuka da lambobin IP, yayin da VPN ke samar da sirrin sadarwa ta yadda masu amfani za su iya kauce wa takunkumin shiga wasu shafuka.
Wani binciken da DW ta gudanar ya nuna cewa kashi 46 cikin 100 na masu amsa tambayoyi a Rasha suna amfani da VPN wajen shiga YouTube, yayin da wasu da dama suka ce har yanzu suna fuskantar matsalolin shiga duk da amfani da VPN.
Masana sun yi karin bayani
Masanin hana shiga shafukan intanet, Michael Klimarev, ya ce tsarin da Roskomnadzor ke amfani da shi ya fi dacewa a kira shi National Domain Name System (NDNS), wanda aka kafa tare da dokar Sovereign Internet Law.
A cewarsa, kamfanonin sadarwa a Rasha dole ne su yi amfani da wannan tsarin maimakon tsarin kasa da kasa, abin da ke bai wa gwamnati damar sarrafa hanyoyin shiga shafukan intanet.

Source: UGC
An cire wasu shafukan labarai
Rahotanni sun nuna cewa an kuma cire sunayen wasu manyan kafafen yada labarai daga tsarin NDNS, ciki har da DW, BBC, Radio Liberty, Facebook da Instagram.
A baya, Roskomnadzor ta fi amfani da fasahar Deep Packet Inspection (DPI) wajen rage saurin shiga wasu shafuka, musamman YouTube, amma masana sun ce sabon matakin na nuna cewa gwamnati ta koma amfani da hanyoyi masu tsauri domin dakile ayyukan dandalan da ba ta da iko a kansu.
An rufe shafukan 'yan Najeriya

Kara karanta wannan
Fitaccen mai barkwanci a Najeriya, AY ya daina zuwa coci, ya fadi abin da ya faru
Ko a 2025, Legit Hausa ta rahoto cewa Gwamnatin tarayya ta rufe shafukan 'yan Najeriya miliyan 13,597,057 a dandalin TikTok, Facebook, Instagram da kuma X.
Rahoton bin Dokar CoP ta 2024 ya nuna cewa ana amfani da wadannan shafukan wajen wallafa abubuwan da basu dace ba.
Hukumar NITDA ta ce goge shafukan zai ƙara tsaron yanar gizo, kuma za ta ci gaba da wayar da kan masu amfani da soshiyal midiya.
Asali: Legit.ng

