Hedkwatar Tsaro Ta Yi Magana kan Raɗe Radin Janye Sojojin Amurka daga Najeriya
- Hedkwatar Rundunar Sojin Najeriya (DHQ) ta ce sojojin Amurka da suka bar Najeriya ba su daga cikin dakarun hadin gwiwa
- Ta ce sojojin Amurka da ke aikin hadin gwiwar tsaro da Najeriya suna nan daram, kuma aiki na ci gaba ba tare da tangarda ba
- DHQ ta bayyana cewa karin sojojin da aka turo domin yin aiki na musamman ne aka janye bayan kammala abin da ya kawo su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hedkwatar Rundunar Soji ta Najeriya (DHQ) ta musanta rahotanni da ke nuna cewa Amurka da janye sojojin da ta turo domin aikin hadin gwiwa na yaki da ta'addanci.
DHQ ta bayyana cewa sojojin Amurka da aka janye daga yankin Tafkin Chadi ba su ne jami'an hadin gwiwa da ke aiki tare da Najeriya ba.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Kotu ta ƙwace Naira miliyan 150 na wani 'dan Majalisar tarayya a Najeriya

Source: Twitter
Daraktan Yada Labarai na DHQ, Manjo Janar Samaila Uba, ne ya bayyana hakan ranar Juma'a, 3 ga watan Yuli, 2026, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.
Uba ya jaddada cewa hadin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka na ci gaba kamar yadda aka tsara.
Sojojin da Amurka ta janye daga Najeriya
Bayanin DHQ ya biyo bayan wani rahoto da ya ce Amurka ta janye sojojinta daga Najeriya bayan kammala wani samame da ya yi sanadin kashe Al Manuki, wanda ake bayyana a matsayin na biyu a jagorancin kungiyar ISIS.
Sai dai Manjo Janar Uba ya ce:
"Abin da ake nufi shi ne karin sojojin da aka turo domin gudanar da aiki na musamman a yankin Tafkin Chadi sune aka janye amma dakarun Amurka da suka kasance a Najeriya tun farko suna nan."
Makomar hadin gwiwar kasashen 2
Manjo Janar Uba ya ce musayar bayanan sirri da aikin hadin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka na ci gaba ba tare da wani sauyi ba.
Ya kara da cewa Najeriya da Amurka na ci gaba da aiki tare wajen dakile da kuma kawar da barazanar ta'addanci da ke shafar kasashen biyu.
DHQ ta bayyana cewa idan bukatar wasu kwarewa, jami'ai ko kayan aiki na musamman ta taso nan gaba, za a samar da su domin cimma manufofin tsaro.

Source: Twitter
Janar Anderson ya yi karin bayani
Rahoton ya nakalto Kwamandan Rundunar Sojin Sama ta Amurka a Afirka, Janar Dagvin R.M. Anderson, yana cewa an kammala aikin da ya sa aka tura karin sojojin Amurka yankin Tafkin Chadi.
Ya ce saboda haka an janye mafi yawan jami'an, amma hadin gwiwar musayar bayanan sirri da gwamnatin Najeriya ta bukata na ci gaba, kamar yadda The Nation ta rahoto.
A cewarsa:
"Aikin da aka gudanar a yankin Tafkin Chadi ya taimaka wajen dakile ayyukan ISIS ba a yankin kadai ba, har ma a duniya baki daya."
Sojojin Amurka sun yi nasara a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta sake fito da nasarorin da ta samu a hare-haren hadin gwiwa da ta kawo Najeriya domin kawo karshen ayyukan ta'addanci.
Wani hadimin shugaban Amurka, Sebastian Gorka ya ce dakarun sojojin kasar sun halaka 'yan ta'adda masu ikirarin jihadi 199 a hari daya kacal a Najeriya.
Gorka ya ce wannan shi ne mafi girman adadin mayakan kungiyar ta'addanci da aka kashe a farmaki guda tun bayan harin 11 ga Satumba, 2001.
Asali: Legit.ng

