Ministan Buhari Ya Rasa Kadararsa bayan Daurin Shekaru 75 a Gidan Kaso
- Kotu ta ƙwace wani katafaren ginin tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, bayan kama shi da laifin badakala
- Babbar Kotun Tarayya ta kuma ba da umarnin ƙwace wasu kadarori huɗu na wucin gadi saboda laifin da ya aikata
- EFCC ta ce har yanzu ba a kwato mafi yawan kuɗaɗen da aka karkatar ba, yayin da Mamman ke ci gaba da zaman gidan yari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon Ministan Wutar Lantarki, Alhaji Saleh Mamman ya rasa wani katafaren gini bayan kama shi da laifin badakala.
Mamman wanda ke zaman hukuncin daurin shekaru 75 a gidan yari saboda karkatar da Naira biliyan 22, ya rasa wani ƙarin katafaren gini da kotu ta ƙwace.

Source: Facebook
Kadarorin Mamman: Umarnin da kotu ta bayar
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta kuma ba da umarnin ƙwace wasu kadarori huɗu na wucin gadi da ake dangantawa da Mamman, cewar The Nation.
Mai shari'a James Omotosho ne ya yanke hukuncin bayan sauraron buƙatar da Hukumar EFCC ta gabatar.
Kadarorin sun haɗa da Walijam Apartments da ke Lobito Crescent, Wuse 2, Abuja, Bloom Luxury Suites Nigeria Limited da ke Unguwan Rimi a Kaduna, da wasu gidaje biyu a Misratah Street.
Sauran kadarorin sun haɗa da A.U.A Plaza da ke kan hanyar Kade a Wuse 2 da ke birnin tarayya Abuja.
Mai shari'a Omotosho ya ba da umarnin ƙwace Walijam Apartments har abada bayan EFCC ta tabbatar cewa an saye shi da kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya.
Sai dai ya ce game da sauran kadarori huɗu, EFCC ba ta kammala tabbatar da cewa Mamman ne ya mallake su ko kuma yake cin moriyarsu ba.
Saboda haka kotun ta ba da umarnin ƙwace su na wucin gadi tare da umartar EFCC ta wallafa sanarwar cikin jaridar ƙasa cikin kwanaki bakwai.

Source: UGC
Kotu ta ba masu korafi dama
Kotun ta ce duk wanda ke da wata korafi kan kadarorin zai iya bayyana a gaban kotu ya nuna dalilin da ya sa ba za a ƙwace su har abada ba.
Kafin yanke hukuncin, mai shari'a ya yi watsi da hujjar lauyan Saleh Mamman, Femi Atteh, cewa kotun ba ta da ikon sake sauraron irin wannan buƙata.
Ya bayyana cewa sashe na 321 na Dokar Gudanar da Shari'ar Laifuka ya ba kotu ikon bayar da umarnin mayar da kadarori ko ƙwace su ko da bayan an yanke hukunci.
Lauyan EFCC, Abba Mohammed, ya ce kotun na da ikon sauraron buƙatar duk da cewa an riga an kammala shari'ar laifin.
Ya tunatar da kotu cewa an tabbatar Mamman ya karkatar da Naira biliyan 22 daga cikin Naira biliyan 33.8 da ake tuhumarsa da karkatarwa.
Ya ce EFCC ta samu nasarar kwato ƙasa da naira biliyan biyu ne kawai duk da umarnin ƙwace kadarori da aka bayar a baya.
Yadda aka cafke tsohon minista a Kaduna
An ji cewa hukumar EFCC ta sanar da cafke tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman, bayan hukuncin kotu kan laifin karkatar da kudade.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce an kama Saleh Mamman ne da misalin karfe 3:30 na safiyar Talata a yankin Rigasa da ke Kaduna.
EFCC ta bayyana cewa ana boye tsohon ministan a cikin wani gida, yayin da aka kama wasu mutum biyu da suke ba shi kariya a gidan.
Asali: Legit.ng

