Gwamna Abba Ya Bayyana Matsayar Kano kan Kafa 'Yan Sandan Jiha
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce Jihar Kano ta shirya tsaf domin kafa rundunar 'yan sandan jiha yayin da ake samun masu aikata laifuffuka a lungu da sako
- Gwamnan ya kuma bayyana irin alaƙar da runduna za ta yi da ta 'Yan Sandan Najeriya idan an kammala kafa ta, ba wai za ta maye gurbinsu ba ne
- Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da goyon bayan duk wata hanya da za ta inganta tsaron Najeriya domin samun sauki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kano – Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa jihar ta shirya domin kafa rundunar 'yan sandan jiha, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen ƙarfafa tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al'umma.
Gwamnan ya bayyana hakan ne ranar Laraba, 22 ga watan Yuli, 2026 yayin ƙaddamar da Kwamitin Haɗin Gwiwa na Hukumomin Tsaro kan Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi da Safararsu, wanda aka gudanar a Fadar Gwamnatin Kano.

Source: Facebook
Jaridar Punch g wallafa cewa a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, Gwamna Yusuf ya ce rundunar 'yan sandan jihar da ake shirin kafawa za ta yi aiki kafada da kafada da Rundunar 'Yan Sandan Najeriya.
Gwamnatin Kano ta shirya kan ƴan sandan jihohi
The Nation ta kawo labarin cewa gwamnatin Kano na ganin rundunar ƴan sandan jihohi za ta cike gurbin da ake da shi ne a bangaren rashin tsaro domin wanzar da zaman lafiya.
Ya ce:
"Rundunar 'yan sandan jiha da ake shirin kafawa za ta kasance mai cike gibin da ke akwai, ba wai mai gogayya da Rundunar 'Yan Sandan Najeriya ba. Dukkaninsu suna da alhakin kare rayuka da dukiyoyi tare da tabbatar da doka da oda."

Kara karanta wannan
Ganduje ya caccaki Kwankwaso kan shirin tattaunawa da 'yan bindiga, ya fadi illarsa
Gwamnan ya ƙara da cewa haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro zai ƙarfafa tattara bayanan sirri, hanzarta ɗaukar matakan kariya da kuma ƙara amincewar jama'a ga jami'an tsaro.
Gwamnan Kano ya nemi hadin kai
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa jihar Kano na da isasshen ƙarfi ta fuskar cibiyoyi, ma'aikata da kuma karfin siyasa domin gudanar da rundunar 'yan sandan jiha idan aka samar da tanadin doka a kundin tsarin mulkin ƙasa.

Source: Facebook
A cewarsa:
"Jihar Kano na da cikakkiyar damar gudanar da rundunar 'yan sandan jiha idan aka samar da tanadin kundin tsarin mulki da ya dace."
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta mara baya ga duk wata halastacciyar hanya da za ta inganta tsarin tsaron Najeriya tare da samar wa 'yan ƙasa muhalli mai aminci.
Majalisar dokokin Kano ta tashi kan rashin tsaro

Kara karanta wannan
2207: Ganduje ya yi wa Obi da Kwankwaso mummunan hasashe, ya hango faduwarsu a Kano
A wani labarin, kun ji cewa majalisar dokokin Kano ta shiga damuwa saboda karuwar hare-hare da ake samu a iyakokin jihar da makwabtanta da ke Arewa maso Yamma, inda ake farmakin mazauna karkara.
Ta fara daukan mataki, musamman wurin binciken yadda ake samun hare-hare domin a samo hanyar warware matsalar baki dayanta a iyakokin jihar, inda ta kafa kwamiti ya binciki yadda ake kashe kudin tsaro.
Kafin a kai ga warware matsalar duka, 'yan majalisar sun kuma bukaci gwamnati ta kara jami'an tsaro da kayan aiki domin dakile yan bindiga da e shigowa su na far wa jama'a a gidajensu da ke iyakokin Kano.
Asali: Legit.ng
