Talaka zai Samu Sauki, Gwamnatin Tinubu Ta Ce a Rage Kudin Man Fetur

Talaka zai Samu Sauki, Gwamnatin Tinubu Ta Ce a Rage Kudin Man Fetur

  • Gwamnatin Bola Tinubu ta buƙaci 'yan kasuwa su rage kudin man fetur bayan farashin danyen mai na duniya ya yi kasa sosai
  • Duk da haka, ministan man fetur ya ce gwamnati ba ta da ikon kayyade farashin fetur a Najeriya bayan cire tallafin mai da aka yi
  • Sai dai ya yi gargadin cewa dole hukumomin da ke kula da harkar mai su hana 'yan kasuwa ci da gumin talakawa ta hanyar kara farashi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta buƙaci 'yan kasuwar man fetur su sauke kudin litar mai saboda raguwar da aka samu kwanan nan a farashin danyen mai na duniya.

Ta kuma jaddada cewa farashin mai yanzu yana ƙarƙashin tsarin kasuwa a bangaren man fetur da aka cire wa gwamnati ikon kayyade farashinsa.

Kara karanta wannan

Tuban muzuru: Malami ya gargadi gwamnati game da karban tuban yan bindiga

Gidan mai da Bola Tinubu
Ana saka man fetur a mota a hagu, shugaba Bola Tinubu a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: Getty Images

Daily Trust ta rahoto cewa karamin ministan albarkatun man fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, ne ya yi wannan kira a ranar Litinin a Abuja.

Dalilin neman rage kudin mai

Kalaman nasa na zuwa ne bayan masu amfani da fetur da sauran masu ruwa da tsaki sun soki abin da suka kira neman riba fiye da kima daga 'yan kasuwar mai duk da raguwar farashin danyen mai a kasuwar duniya.

Ministan ya ce sukin rikicin siyasa tsakanin Iran da Amurka ya haifar da raguwar farashin danyen mai a duniya, wanda a zahiri ya kamata ya jawo saukar farashin fetur da sauran kayayyakin man fetur a cikin gida.

“Bayan rage tashin hankali tsakanin Iran da Amurka, mun yi tsammanin za a ga raguwar farashin mai da sauran kayayyakin man fetur. Amma har yanzu hakan bai faru ba,”

In ji Lokpobiri.

Ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa tsarin kasuwa zai kai ga raguwar farashi, amma ya jaddada cewa dole masu sa ido su tabbatar da cewa ba a yi anfani da tsarin cire tallafi wajen cutar da masu sayen mai ba.

Kara karanta wannan

Sarkin Zazzau ya yi kira a rage kudin da ake kashewa yayin bukukuwa

Mutane a gidan mai
Yadda jama'a ke sayen fetur a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ba a kayyade farashin mai ba

Lokpobiri ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya ba ta da ikon kayyade ko rage farashin fetur tun bayan cire tallafi a bangaren man fetur ƙarƙashin dokar masana’antar man fetur ta 2021.

A cewarsa, farashin mai yanzu yana kasancewa ne ta hanyar tsarin kasuwa, inda gasa, samar da shi da buƙatar shi ne manyan abubuwan da ke tasiri kan farashin gidajen mai.

Sai dai ya ce NMDPRA na da alhakin sa ido kan masu harkar mai da kuma tabbatar da kare masu amfani daga karin farashi ba bisa ka'ida ba.

Dangote ya rage kudin mai

A wani labarin, mun kawo muku cewa matatar Dangote da ke Legas ta sanar da rage kudin litar man fetur da N50 a makon da ya wuce.

Bayan rage kudin litar mai, farashin fetur a matatar Dangote ya sauka daga N1,175 zuwa N1,125 ga manyan 'yan kasuwa da ke saye a wajen shi.

Rahotanni sun bayyana cewa Dangote ya sauke farashin ne bayan rikicin Gabas ta Tsakiya ya lafa sakamakon sulhun Amurka da Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng