Sauki Ya Zo: Matatar Dangote Ta Zaftare Farashin Man Fetur
- Ana sa ran za a samu sauki a gidajen mai bayan matatar Dangote ta rage farashin da take sayar da man fetur ga 'yan kasuwa
- Matatar Dangote ta rage farashin da take sayar da litar man fetur ga 'yan kasuwa 'yan kwanaki bayan ta dauki irin wannan mataki
- Hakazalika, matatar ta kawo sabon tsarin bayar da damar sayen man fetur ga dukkanin 'yan kasuwar da suka cancanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Matatar man Dangote da ke a jihar Legas ta rage farashin sayar da man fetur ga 'yan kasuwa.
Matatar ta Dangote ta rage farashin da take sayar da man fetur daga Naira 1,125 kan kowace lita zuwa Naira 1,075 kan kowace lita.

Source: Facebook
Sabon farashin na ragin Naira 50 kan kowace lita, shi ne karo na biyu da aka samu ragi a cikin kwanaki bakwai kacal, inda a baya aka rage daga Naira 1,175 zuwa Naira 1,125 kan kowace lita.
Matatar Dangote ta rage farashin fetur
Wannan sabon sauki ya nuna ragi na Naira 50 ko kashi 4.4 cikin 100 daga farashin da matatar take sayarwa a baya.
Binciken da aka gudanar a ranar Alhamis, 2 ga watan Yulin 2026 ya nuna cewa matatar ta kuma daidaita farashin loda man ta hanyar teku zuwa Naira 1,075 kan kowace lita.
Hakan ya soke bambancin farashin da ke tsakanin sayar da man ga masu saya ta jiragen ruwa da kuma sayarwa kai tsaye daga matatar na baya.
Yaushe ragin zai fara aiki?
Wani babban jami’i a matatar man fetur ta Dangote, wanda ya bukaci a sakaya sunansa saboda ba a ba shi ikon yin magana da manema labarai ba, ya ce sabon tsarin farashin ya fara aiki nan take.
“Matatar ta rage farashin man fetur kai tsaye daga Naira 1,125 kan kowace lita zuwa Naira 1,075 kan kowace lita. An kuma daidaita farashin loda man ta teku zuwa Naira 1,075 kan kowace lita."
"Wannan na cikin kokarin matatar na ganin kayayyaki sun fi samuwa kuma a kan farashi mai kyau a kasuwa." inji shi

Source: Facebook
Matatar Dangote ta kawo sabon tsari
Bayan haka, jami’in ya bayyana cewa matatar ta dakatar da tsarin hadin gwiwa na kungiyar 'yan kasuwa mambobi 20, inda ta bude damar loda kayayyaki ga daukacin 'yan kasuwar da suka cancanta.
Bincike a shafin petroleumprice.ng shi ma ya tabbatar da sabon farashin na Naira 1,075 kan kowace lita a matatar ta Dangote.
Wannan ragi na baya-bayan nan zai iya tilasta wa gidajen mai daidaita farashinsu na sayarwa zuwa kasa a kwanaki masu zuwa, musamman ma wadanda ke samo kayayyaki kai tsaye daga matatar.
Gwamnati ta bukaci a rage farashin fetur
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta mika bukatarta ga 'yan kasuwar man fetur kan farashin da suke sayar da shi.
Gwamnatin tarayya ta buƙaci 'yan kasuwar man fetur su sauke kudin litar mai saboda raguwar da aka samu a farashin danyen mai na duniya.
Ta kuma jaddada cewa farashin mai yanzu yana ƙarƙashin tsarin kasuwa a bangaren man fetur da aka cire wa gwamnati ikon kayyade farashinsa.
Asali: Legit.ng

