Trump Ya Sake Zama kan Yiwuwar Koma wa Yaƙi da Iran

Trump Ya Sake Zama kan Yiwuwar Koma wa Yaƙi da Iran

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya fara nazarin yiwuwar sake kai wa Iran manyan hare-haren soja yayin da ƙasashen ke ci gaba kai hari
  • Ana zargin Trump ya tattauna da manyan hafsoshin tsaron Amurka kan ko za a dakatar da tattaunawar nukiliya da Iran ko a koma yaƙi
  • Iran ta ce ba za ta gana da manyan wakilan Amurka ba sai an fara warware batutuwan yarjejeniyar tsagaita wuta da ke kunshe a daftarin sulhu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

United States of America – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya fara nazari da duba yiwuwar sake ƙaddamar da manyan hare-haren soja kan Iran.

Sai dai kawo yanzu, Shugaban ya yanke shawarar ci gaba da bai wa tattaunawar diflomasiyya dama ko za a warware ƙalubalen da ke gabansu.

Kara karanta wannan

Amurka ta samu nasara mafi girma cikin shekaru 25 a farmakin da ta kawo Najeriya

Shugaban Amurka yazauna da manyan jami'an gwamnatinsa
Shugaban Amurka Donald Trump a wani taro a kasarsa Hoto: Donald J Trump
Source: Twitter

Rahoton da ya kebanta ga Wall Street Journal ya bayyana cewa Trump ya gudanar da tattaunawa da Sakataren Tsaro na Amurka, Pete Hegseth.

Trump ya gana da jami'ansa

The Times of India ta wallafa cewa Trump ya gana da shugaban hafsoshin sojin ƙasar, Janar Dan Caine, domin duba ko Amurka za ta janye daga tattaunawar nukiliya da Tehran ta koma kai hare-haren soja.

An ce tattaunawar ta fi mayar da hankali ne kan yiwuwar Amurka ta kammala aikin ta hanyar sake kai wani sabon jerin hare-hare kan Iran.

Sai dai jami'ai sun bayyana cewa Trump na ganin sabon yaƙi a wannan lokaci zai iya kawo cikas ga tattaunawar da ake yi, tare da rage damar cimma yarjejeniyar da za ta dakile shirin nukiliyar Iran.

Rahoton ya kuma ce Donald Trump ya sanar da masu ba shi shawara cewa a shirye yake ya bai wa tattaunawar ƙarin lokaci, har ma bayan wa'adin ranar 18 ga Agusta, 2026 da aka tsara domin cimma yarjejeniya.

Kara karanta wannan

Fada zai dawo: Trump ya yi gargadi mai tsauri kan Iran duk da maganar sulhu

Duk da haka, an ce shugaban na goyon bayan kai farmaki cikin gaggawa idan Iran ta karya yarjejeniyar da ke tsakanin ɓangarorin biyu.

Martanin Iran kan Amurka

Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, ya bayyana cewa gwamnatin Trump za ta ci gaba da tattaunawa, amma har yanzu tana da zaɓuka masu yawa idan diflomasiyya ta gaza.

Iran ta ce babu batun tattauna wa da Amurka sai an duba yarjejeniyarsu da kyau
Shugaban kasar Iran, Masoud Pazeshkian Hoto: Masoud Pazeshkian
Source: Getty Images

A halin yanzu, wakilan Trump kan harkokin Gabas ta Tsakiya, Steve Witkoff da Jared Kushner, sun isa Doha domin wata sabuwar tattaunawa ta kai tsaye ba tare da ɓangarorin sun haɗu fuska da fuska ba, inda Qatar ke shiga tsakani.

Sai dai har yanzu ana samun sabani kan wasu muhimman batutuwa, ciki har da shirin nukiliyar Iran da kuma wasu buƙatun Tehran da suka shafi zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigin Hormuz.

A ranar Talata 30 ga watan Yuni, 2026, Iran ta sanar da cewa ba za ta gana da manyan wakilan Amurka da suka isa yankin ba sai an warware sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma makonni biyu da suka gabata.

Ana zargin 'dan Amurka da taimakon Iran

Kara karanta wannan

Kungiyar CAN ta 'karyata' Trump kan batun kisan Kiristoci a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Isra'ila ta kama wani matashi ɗan ƙasar Amurka mai shekaru 20 da haihuwa kan zargin yi wa hukumomin leƙen asirin Iran aiki da zummar durkusar da ita a yakin da ake yi.

Isra'ila na zargin matashin da ɗaukar hotuna da tattara bayanan sirri kan muhimman wurare a cikin Isra'ila, inda aka ce Iran ce ke ba shi kudi yana yi mata wannan aiki domin samun karin bayanan cikin kasar.

Bayan binciken farko, rundunar 'yan sandan Isra'ila ta ce za a gurfanar da shi gaban kotu a nan gaba kadan, inda ta ce za ta cigaba da kakkabe irinsu da ake zargin suna yi wa kasar Iran aikin leken asiri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng