Tsohon Hadimin Shugaban Ƙasa Ya Yi wa Gwamna Abba Kabir Tayin Mata

Tsohon Hadimin Shugaban Ƙasa Ya Yi wa Gwamna Abba Kabir Tayin Mata

  • Reuben Abati ya shawarci Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya nemi sabuwar mata daga cikin matan da suke aiki
  • Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa ya bayyana matan kafar a Abuja da Legas a matsayin masu ilimi, kyau, basira da kishin aiki
  • Abati ya ce zama matar gwamna dama ce mai kyau, yana mai cewa ya kamata Abba Kabir Yusuf ya yi la'akari da shawararsa domin taimako yana farawa daga gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Fitaccen dan jarida kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, Reuben Abati, ya yi wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf tayin mata.

Tsohon hadimin shugaban kasar ya yi barkwanci inda ya ba shi shawarar zai nemo masa sabuwar mata bayan samun matsala da daya tsohuwar matarsa.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya yi magana da Abba Kabir ya 'saki' matarsa a bainar jama'a

An yi wa Abba Kabir tayin mata
Diyar Rabiu Kwankwaso da ake kira Zainab da gwamna Abba Kabir. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne yayin shirin Arise Morning Show, inda ya ce kafar yada labaran na da mata masu kyau, ilimi, basira da kwazo wajen gudanar da ayyukansu.

Abati ya shawarci gwamnan da ya duba cikin matan da ke aiki da gidan talabijin na Arise News domin samun wadda za ta iya zama sabuwar matar Gwamna Abba Kabir.

Abati ya fadi halayen matan Arise News

Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa ya ce akwai mata da dama a cikin ma'aikatan Arise News da za su iya dacewa da gwamnan.

A cewarsa, matan da ke aiki da kafar a Abuja da Legas suna da kyawawan halaye da suka hada da lafiya, kyau, ilimi da hazaka.

Abati ya bayyana cewa:

"Yayin da Gwamnan Kano, Yusuf, ke neman sabuwar mata, ya kamata ya duba wajen Arise News. Muna da mata masu koshin lafiya, kyau, ilimi, basira da himma a cikin iyalinmu, a Abuja da Legas."

Kara karanta wannan

Kano ta ɗauki zafi, Gwamna Abba ya yi kalaman da ake zargin ya nuna ya saki matarsa

Abati ya yi wa gwamna Abba tayin mata
Dan jarida, Ruben Abati da gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Ruben Abati.
Source: Instagram

Dama ce zama matar Gwamna - Abati

Abati ya kara da cewa zama matar gwamna wata dama ce mai kyau, don haka ya kamata Abba Kabir Yusuf ya yi la'akari da shawararsa domin samun matar da ta dace da shi.

Ya ce taimako yana farawa ne daga gida, saboda haka yake ganin ya dace gwamnan ya fara duba cikin ma'aikatan Arise News.

Ya ce:

"Zama matar gwamna dama ce mai kyau matuka. Taimako yana farawa ne daga gida, shi ya sa nake ba da shawarar namu."

Wannan shawara ta Abati ta zo ne cikin barkwanci, inda ya nuna cewa Arise News na iya zama wajen da gwamnan zai samu sabuwar mata.

Dalung ya magantu kan rikicin auren Abba Kabir

An ji cewa tsohon minista Solomon Dalung ya soki Gwamna Abba Kabir Yusuf kan yadda ya bayyana batun rabuwa da matarsa wanda ya kawo maganganu a Najeriya.

Kara karanta wannan

"Shugaba Tinubu ba zai lamunci a taɓa mutuncin marigayi Buhari ba"

Tsohon ministan ya ce babu laifi gwamnan ya raba aure, amma bai kamata ya yi amfani da kalaman da za su rage mutuncin matar tasa ba.

Dalung ya gargadi Abba cewa siyasa da sauyin kawance za su iya gushewa, amma 'ya'yansa za su ci gaba da tunawa da lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.