Minista Ka Iya Rasa Kujerarsa, an Kirayi Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta Ɓaci
- Wata ƙungiyar fararen hula a Najeriya ta nuna damuwa game da yadda halin kiwon lafiya yake a kasar
- Ta ba Shugaban kasa, Bola Tinubu shawarar yadda zai kawo gyara a fannin lafiya tare da ɗaukar matakai
- Ƙungiyar ta ce ƙarancin likitoci, ficewar ƙwararrun ma'aikata ƙasashen waje, yawan yajin aiki da ƙarancin kuɗaɗe sun jefa tsarin lafiya cikin mawuyacin hali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Wata ƙungiyar fararen hula mai suna Coalition of Concerned Nigerians on Health Reform ta koka game da bangaren kiwon lafiya.
Ƙungiyar ta bukaci Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a fannin lafiya tare da cire Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama'a, Farfesa Muhammad Ali Pate, daga mukaminsa.

Source: Twitter
Hakan na cikin wata sanarwa mai taken "Enough Is Enough: Declare a State of Emergency in Nigeria's Health Sector Now," cewar The Sun.
Matsalolin da bangaren lafiya ke ciki
Shugaban kungiyar, Muniretu Isa, ya ce tsarin kiwon lafiyar Najeriya ya kai wani mataki mai hatsari.
Ya bayyana cewa hanyoyin manufofin gwamnati da ake amfani da su a yanzu ba su isa su magance matsalolin da ke ci gaba da ta'azzara ba.
Ƙungiyar ta bayyana cewa ministan ya gaza magance matsalolin da suka addabi tsarin kiwon lafiya a Najeriya, saboda haka ta kaɗa ƙuri'ar rashin amincewa da shugabancinsa.
Ya ce miliyoyin 'yan Najeriya na ci gaba da fuskantar jinkirin samun magani, mace-macen da za a iya kauce wa da kuma ƙarancin samun ingantattun ayyukan kiwon lafiya.
Ƙungiyar ta ce ma'aikatan lafiya sun yi ƙasa ƙwarai idan aka kwatanta da yawan jama'ar ƙasar, inda ta ce likitoci masu lasisi kusan 55,000 ne kawai ke kula da mutane sama da miliyan 220.
Ta ce ci gaba da ficewar likitoci da sauran ƙwararrun ma'aikatan lafiya zuwa ƙasashen waje ya bar asibitoci da ƙarancin ma'aikata, lamarin da ke haddasa dogon lokaci kafin marasa lafiya su samu kulawa.

Source: Twitter
Kungiya ta magantu kan karancin likitoci
Ƙungiyar ta ƙara da cewa hakan na janyo jinkirin ba da agajin gaggawa da kuma rage damar samun ƙwararrun likitoci, musamman a yankunan karkara masu fama da ƙarancin ma'aikata da kayan aiki.
Ta kuma danganta yawan rikice-rikicen ƙwadago a fannin lafiya da ƙarancin albashi, rashin biyan wasu alawus, jinkirin albashi, ƙarancin ɗaukar ma'aikata da kuma munanan yanayin aiki.
A cewarta, tsofaffin kayan aikin likitanci, lalacewar gine-ginen asibitoci da gazawar gwamnati wajen aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma da ƙungiyoyin ma'aikata suna ƙara dagula al'amura.
Ƙungiyar ta yi gargadin cewa yawan yajin aiki da barazanar sake shiga yajin aiki na ci gaba da tura tsarin kiwon lafiyar Najeriya kusa da rugujewa, cewar Daily Post.
'Tinubu ya cancanci tazarce' - Ali Pate
An ji cewa ministan lafiya, Muhammad Ali Pate ya yi bayanin abin da ya sa yake ganin Shugaba Bola Tinubu ya cancanci tazarce a zaben 2027.
Ali Pate ya ce Shugaba Tinubu ya samu nasarori da dama ciki har da sama wa matasa ayyukan yi a shekaru uku da ya kwashe a kan madafun iko.
Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da manema labarai a ƙarshen mako bayan zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa.
Asali: Legit.ng


