Lafiya: Ministan Tinubu Ya Shiga Jerin Mutane 100 Mafi Muhimmanci a duniya
- Ministan Lafiya, Farfesa Ali Pate, ya samu yabo daga masana, bayan an saka shi cikin jerin manyan mutane 100 a fannin lafiya a duniya
- Kungiyar GHC ta yaba da rawar da ya taka wajen gyaran fannin lafiya da kokarinsa na bunkasa samar da magunguna a cikin gida
- An kuma bukaci ya warware rikice-rikicen da ke cikin fannin lafiya ta hanyar adalci da mutunta dukkan ma’aikatan lafiya a kasar nan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Ministan lafiya, Farfesa Mohammed Ali Pate, ya samu gagarumin yabo daga manyan masana a harkar lafiya da magunguna a Najeriya.
Ali Pate ya samu yabon ne bayan amincewar da aka yi masa a matsayin daya daga cikin manyan mutane 100 mafi tasiri a fannin lafiya a duniya.

Asali: Twitter
Ministan lafiya ya sha ruwan yabo
Yabon ya fito ne daga hadin gwiwar kamfanoni ciki har da Geneith Pharmaceuticals', kamar yadda Tribune ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Wannan karramawa da aka yi maka yana nuna irin tasirin da ka yi wajen sauya tunanin duniya game da harkokin lafiya.
“Jagorancin ka na sauyi da irin gudunmuwar da ka bayar sun kai Najeriya cikin taswirar lafiya ta duniya.”
- Cewar sanarwar
An karrama Farfesa Pate ne a daidai lokacin da ake kan kokarin sake fasalin tsarin lafiyar Najeriya, da nufin kara samun saukin kula da lafiya a matakin farko da yakar cututtuka.
GHC ta tunatar da irin nasarorin da ya samu lokacin yana Sakataren Hukumar Kula da Lafiyar Farko (NPHCDA), inda ya sake karfafa ayyukan asibitocin matakin farko da tura ma’aikatan lafiya yankunan karkara.

Asali: Twitter
Gudunmawar Ali Pate a bangaren lafiya
An kuma bayyana rawar da ya taka wajen hanzarta samar da rigakafin zazzabin cizon sauro, cewar The Nation.
GHC ta kara da yabawa Farfesa Pate bisa goyon bayansa ga samar da magunguna a gida, tana bayyana hakan a matsayin babbar sauyi a tsarin lafiya.
Sanarwar ta ce:
“Wannan mataki yana da matukar muhimmanci wajen yaki da zazzabin sauro, wanda ke haddasa kusan kashi 65% na ziyartar asibiti.
“Ta hanyar bai wa masana'antun gida fifiko, kana karfafa ikon lafiyar kasa da tsare-tsaren samar da magani."
Sai dai kuma kungiyar ta yi amfani da damar wajen jawo hankali kan rikice-rikicen da ke tunkarar bangaren lafiya.
“Muna da tabbacin zaka mutunta doka kuma ka tabbatar duk ma’aikatan lafiya sun samu hakkokinsu."
- A cewar sanarwar
Kungiyar ta kuma bukaci hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban a fannin lafiya, tana mai cewa hakan ne sirrin nasarar tsarin lafiya a kasashen da suka ci gaba.
Tinubu ya kawo shirin haihuwa kyauta ga mata
Kun ji cewa ministan lafiya da walwalar jama'a, Farfesa Muhammad Ali Pate ya bayyana shirin gwamnati a kan matan Najeriya.
Ministan ya fadi haka a wani taro na hadin gwiwa da ake yi duk shekara inda ya ce shirin zai rage mutuwar mata.
Pate ya ce alkaluma sun nuna yadda ake asarar rayukan mata da jariransu yayin haihuwa, shi ya sa aka dauki matakin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng