Bayan Shan Wuta, Mayakin ISWAP na kan Kogi Ya Mika Wuya ga Jami’an Sojoji
- Rahotanni suka ce wani da ake zargin ɗan ISWAP ne ya miƙa wuya ga sojoji a Damasak d ake jihar Borno
- Wanda ya miƙa wuya ya ce ya tsere daga sansanin 'yan ta'adda a yankin Tafkin Chadi saboda hare-haren sama da sojoji ke kai wa
- Sojoji sun killace shi ana yi masa tambayoyi da tattara bayanan sirri, yayin da jami'an tsaro suka ce hakan na nuna raunin 'yan ta'adda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Damasak, Borno - Rahotanni sun tabbatar da cewa sojoji sun yi arangama da wasu yan ta'addan ISWAP a jihar Borno.
Wani da ake zargin mayaƙin ISWAP ne, wanda aka horar da shi kan yakin tukin kwale-kwalen da kuma sarrafa babbar bindigar Dushka, ya miƙa wuya.

Source: Twitter
Majiyar Zagazola Makama ta tabbatar da cewa mayakin ya mika wuya ga dakarun Runduna ta 5 a Damasak da ke ƙaramar hukumar Mobbar a Borno.

Kara karanta wannan
Jirgin sojojin Najeriya ya far wa yan bindiga kimamin 200, ya musu gagarumar illa a Neja
Yadda dan ISWAP ya mika wuya
Majiyoyin leƙen asiri sun shaida cewa mutumin ya miƙa wuya ga dakarun soji da misalin ƙarfe 9:00 na safiyar ranar 1 ga Yulin 2026.
Binciken farko ya nuna cewa mutumin ya tsere daga sansanin 'yan ta'adda da ke ƙauyen Barra a yankin Tafkin Chadi kusa da Dogon Chukwu, wanda ake zargin yana ƙarƙashin jagorancin wani shugaban 'yan ta'adda mai suna Abu Ubeida.
A yayin tambayoyin farko, mutumin ya bayyana cewa an horar da shi tukin kwale-kwalen yaƙi, sannan yana amfani da babbar bindigar Dushka wajen kai hare-haren ta'addanci a yankin Tafkin Chadi.

Source: Original
Musabbabin mika wuyan dan ta'addan a Borno
A cewar majiyoyin, ya ce ya yanke shawarar tserewa ne saboda ci gaba da hare-haren jiragen yaƙin sojoji kan sansanonin 'yan ta'adda, waɗanda suka kawo cikas ga ayyukansu tare da tsananta musu rayuwa.
Bayan ya miƙa wuya, sojoji sun killace shi bisa tsarin aiki na rundunar, sannan suka ba shi abinci da kulawar lafiya.
A halin yanzu yana hannun dakarun soji domin ci gaba da tantance shi, yi masa ƙarin tambayoyi na leƙen asiri da kuma kammala sauran matakan gudanarwa.
Majiyoyin tsaro sun ce wannan miƙa wuya na nuna tasirin ci gaba da hare-haren sama da na ƙasa da sojoji ke kai wa, waɗanda ke raunana ƙarfin 'yan ta'adda tare da ƙarfafa wasu daga cikinsu su fice daga ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya a Arewa maso Gabas.
Yadda ISWAP suka sace dalibai a Borno
Mun ba ku labarin cewa 'yan ta'addan kungiyar ISWAP sun kutsa wata makarantar sakandare a Borno inda suka sace daliban da ke rubuta jarabawar NECO.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Borno. Nahum Daso, ya bada bayanai kan yadda 'yan ta'addan suka sace daliban.
Nahum Daso ya bayyana cewa 'yan ta'addan sun badda kama ne a lokacin da ake cin kasuwar garin da aka sace daliban wanda ya tayar da hankula.
Asali: Legit.ng
