'Yan Bindiga Sun Kwashi Kashinsu a Hannu bayan Kai Hari a Katsina
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-hare a wasu kauyukan karamar hukumar Charanchi da ke jihar Katsina
- Jami'an tsaro sun garzaya zuwa wurin da lamarin ya auku bayan samun labarin ta'asar da 'yan bindigan suka aikata a kauyukan guda biyu
- Saurin kai daukin da jami'an tsaron suka yi ya jawo sun samu nasarar dakile harin tare da kwsto dabbobi da dama da 'yan bindigan suka sace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta samu nasarar dakile wani harin da'yan bindiga suka kai.
Jami'an tsaron sun sanar da gano dabbobi guda 117 bayan wani aikin hadi na tsaro ya dakile yunkurin satar shanu da wasu da ake zargi 'yan bindiga ne suka yi a karamar hukumar Charanchi.

Source: Original
Jaridar Daily Trust ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta hannun jami’an hulda da jama’a, DSP Abubakar Sadiq-Aliyu.
'Yadda jami'an tsaro suka fatattaki 'yan bindiga
Ya ce aikin ya biyo bayan sahihan bayanan sirri ne cewa 'yan bindiga sun kai hari kauyukan Saburu da Billiri a ranar Talata, 30 ga watan Yunin 2026 tare da kwashe dabbobi da dama.
DSP Abubakar ya ce DPO na Charanchi ya gaggauta hada jami'an tsaro na musamman tare da hadin gwiwar sojoji da kuma jami'an KSCWC domin bin sawun wadanda ake zargin da suka tsere.
A cewar kakakin rundunar 'yan sandan, hadin gwiwar dakarun tsaron sun toshe hanyoyin da 'yan bindigan ke bi domin tserewa, lamarin da ya kai ga fafatawa mai zafi.
“Karfin makamai da kuma hadin gwiwar jami’an sun tilasta wa ‘yan bindigan yin watsi da dabbobin da suka sata, sannan suka tsere zuwa cikin daji."
- DSP Abubakar Sadiq-Aliyu
An kwato dabbobi a hannun 'yan bindiga
Kakakin 'yan sandan ya bayyana cewa jami'an tsaron sun gano shanu 43 da tumaki 74, wanda hakan ya sa adadin dabbobin da aka ceto ya kai 117.

Kara karanta wannan
Jirgin sojojin Najeriya ya far wa yan bindiga kimamin 200, ya musu gagarumar illa a Neja
Ya kara da cewa ana ci gaba da kokarin gano tare da kamo wadanda ake zargin da suka ranta ana kare.

Source: Facebook
Yayin da yake yaba wa jami'an saboda jajircewa da kwarewa, kwamishinan 'yan sanda, Aliyu Umar-Fage, ya yaba da hadin gwiwa tsakanin 'yan sanda, sojoji da kuma KSWC, inda ya bayyana wannan alaka a matsayin silar samun nasarar aikin.
Ya sake jaddada kudurin rundunar na kare rayuka da dukiyoyi a fadin Jihar Katsina, sannan ya bukaci mazauna yankin da su ci gaba da marawa jami'an tsaro baya.
'Yan bindiga sun kashe babban limami
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kao harin da ya yi sanadiyyar rasa ran babban limami a jihar Sokoto.
'Yan bindigan sun kai harin ne a Talluje da kuma kauyen Chofi, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar wasu mutane biyu.
Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun kai hare-hare na hadin gwiwa a dukkan kauyukan biyu a lokaci guda, inda suka rika harbi ba kakkautawa.
Asali: Legit.ng
