Tinubu Ya Fara Gina Babbar Hanya, za Ta Ratsa Jihohin Arewa 5

Tinubu Ya Fara Gina Babbar Hanya, za Ta Ratsa Jihohin Arewa 5

  • Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar da aikin na hanyar Akwanga zuwa Jos tare da buɗe hanyar cikin garin Akwanga a jihar Nasarawa
  • A bayanin da ya yi, gwamna Abdullahi Sule ya ce an gina hanyar cikin garin Akwanga ba tare da karɓar bashin banki ba
  • Tinubu ya ce aikin zai ƙarfafa haɗin kai da bunƙasa tattalin arziƙi, musamman lura da cewa hanyar za ta ratsa jihohin Arewa akalla biyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Nasarawa - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ƙaddamar da aikin gina babbar hanyar Akwanga zuwa Jos da ta hada jihohi biyar.

Bayan kaddamar da hanyoyin, Bola Tinubu ya buɗe hanyar garin Akwanga da aka faɗaɗa da kuma gadar ƙasa da gwamnatin jihar Nasarawa ta gina.

Kara karanta wannan

Minista ya fadi abin da ke bata masa rai game da yan kasa kan gwamnatin Tinubu

Shugaban APC da wasu gwamnoni
Shugaban APC wajen kaddamar da aikin titi. Hoto: All Progressive Congress
Source: Facebook

APC ta wallafa a X cewa shugaban jam’iyyar, Farfesa Nentawe Yilwatda ne ya wakilci shugaba Bola Tinubu wajen ƙaddamar da ayyukan a Akwanga ranar Laraba.

Bayanin Gwamnan jihar Nasarawa

Da yake jawabi, Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana cewa aikin hanyar cikin garin Akwanga na ɗaya daga cikin manyan nasarorin gwamnatinsa.

Ya ƙara da cewa an biya duk waɗanda ayyukan suka shafa cikakkiyar diyya kan kadarorinsu, lamarin da ya sa suka ba da haɗin kai wajen aiwatar da aikin.

Gwamnan ya gode wa Shugaban APC na ƙasa bisa haɗa buɗe ayyukan cikin jadawalin ziyararsa tare da ƙaddamar da aikin hanyar Akwanga zuwa Jos.

Bola Tinubu ya yabi gwamna Sule

A nasa jawabin, Shugaba Tinubu ya yabawa Gwamna Sule kan aiwatar da waɗannan ayyuka a Akwanga, yana mai cewa gina irin waɗannan manyan ayyuka a ƙaramar hukuma, ba a babban birnin jiha kaɗai ba, alama ce ta nagartaccen shugabanci.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS sun cafke mutum 5 na kusa da tsohon gwamna kan yunkurin juyin mulki

Ya ce aikin ya samo asali ne daga haɗin gwiwar gwamnatin tarayya da ta jihar, kuma zai haɗa Abuja da Akwanga da kuma Makurdi da Akwanga.

Tinubu ya ce hanyar za ta ƙara wa APC ƙarfi a jihar a zaɓuɓɓuka masu zuwa, sannan ya yaba wa Gwamna Sule bisa amincewa da tasirin sauye-sauyen tattalin arziƙin gwamnatinsa wajen ƙara kuɗin shiga na jihar.

Hanyar da aka kaddamar a nasarawa
Babbar hanyar da gwamnan Nasarawa ya gina. Hoto: All Progressive Congress
Source: Facebook

Hanyar ta ratsa jihohi 5

Shi ma Ministan Ayyuka, David Umahi, ya ce manyan ayyukan hanyoyin gwamnatin Tinubu na shirin Renewed Hope an tsara su ne domin haɗa dukkan sassan ƙasar, bunƙasa tattalin arziƙi da ƙarfafa haɗin kan ƙasa.

Umahi ya bayyana cewa hanyar Akwanga zuwa Jos ita ce sashe na farko na mataki na farko na babbar hanyar Akwanga zuwa Maiduguri a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.

Ya ce aikin zai ratsa jihohin Nasarawa, Kaduna da Plateau, kuma yana cikin wata babbar hanya mai tsawon kilomita 700 daga Akwanga zuwa Maiduguri ta Kaduna, Jos, Bauchi, Gombe da Biu.

Ma'aikatar yada labarai ta wallafa cewa ministan ya ƙara da cewa an riga an fara aikin sashen Gombe zuwa Biu, yayin da ake tsara sauran sassan Jos zuwa Bauchi, Bauchi zuwa Gombe da Biu zuwa Maiduguri domin ba da kwangila.

Kara karanta wannan

Zargin badakalar N400m: Atiku ya bukaci Tinubu ya kori shugaban ma'aikatansa

Tinubu zai ciwo bashin $1.25bn

A wani labarin, kun ji cewa bankin duniya ya yarda zai ba gwamnatin Najeriya bashin kudi har dala biliyan 1.25 domin wasu muhimman ayyuka.

A ranar Laraba, 1 ga Yulin shekarar 2026 bankin ya sanar da cewa zai ba Najeriya rancen kudin da zai kai har kusan Naira tiriliyan 2.

An bayyana cewa gwamnatin Najeriya za ta yi ayyukan da suka shafi inganta wutar lantarki, samar da ayyuka, harkokin noma da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng