Hisbah Ta Yi Maganar Samawa Nafisat Abdullahi Miji domin Ta Yi Aure
- Rahoto ya nuna cewa hukumar Hisbah ta Kano ta buƙaci wani mai hannu da shuni ya nemi auren jarumar Kannywood, Nafisat Abdullahi
- Mataimakin babban kwamandan Hisbah, Dr Mujahid Aminuddeen, ya ce hakan zai zama babbar gudunmuwa ga addinin Musulunci
- Ya ce maimakon zagi da cin mutuncin fitattun mata da ke yin irin waɗannan kalamai, ya kamata a taimaka musu ta hanyar aurensu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Mataimakin hukumar Hisbah na jihar Kano, Dr Mujahid Aminuddeen ya yi magana kan sukar aure da jaruma Nafisat Abdullahi ta yi.
Maimakon caccakar jarumar, jami'in Hisbah ya baukkaci a mayar da hankali wajen samawa mata irinsu mazajen da za su aure su.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro bayanan da Dr Mujahid Aminudden ya yi ne a wani sako mai dauke da muryar shi da shafin Arewa Updates ya wallafa a Facebook.
Batun samawa Nafisat miji
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi kira da a samu wani nagartaccen mai hannu da shuni ya fito ya nemi auren jarumar Kannywood, Nafisat Abdullahi.
Rahotanni sun nuna cewa mataimakin shugaban hukumar, Dr Mujahid Aminuddeen ne ya bayyana hakan ranar Laraba,1 ga watan Yulin 2026 a birnin Kano.
Ya bayyana cewa jihadi ne a samu wani namiji ya fito ya auri jarumar, saboda aure yana cika rabin addinin mutum kamar yadda Musulunci ya koyar.
Magana kan sukar Nafisat
Dr Dr Mujahid Aminuddeen ya ce duk lokacin aka samu irin waɗannan fitattun mata sun fito sun yi magana kamar irin kalaman da Nafisat ta yi, bai kamata a mayar da hankali wajen zagi da ɓata masu suna ba.
A cewarsa, maimakon hakan a samu wani nagartaccen mai kuɗi da zai iya riƙe ta ya fito ya nemi aurenta domin hakan ba ƙaramin jihadi ya yi wa Musulunci ba.
A bayanan da ya yi, ya ce mafi yawa idan mata suna irin kalaman Nafisat, to sun yi iya ƙoƙarinsu ne na samun aure sun rasa.

Source: Getty Images
Magana kan zaman aure
Dr Mujahid Aminuddeen ya kara da cewa ba a yanke hukunci kan halin zaman gidan miji saboda abin da wani ya aikata, domin a cewarsa, ba kowa ne ya ke bin dokar Allah ba a cikin maza.
Ya kara da cewa wasu mazan, har ma da wasu mata, ba su yin abin da ya kamata wajen alaka da abokan zaman su, amma hakan ba lasisin sukar zaman aure gaba daya ba ne.
Ya kara da cewa aure sunnar Annabi SAW ce,saboda haka babu wani dalilin da zai saka mutum ya rika sukar abin da addini ya tabbatar da shi.
Maganar Nafisat kan aure
A wani labarin, mun kawo muku cewa jarumar Kannywood, Nafisat Abdullahi ta caccaki mata kan yadda suke daukar zaman aure.
Ta bayyana cewa zaman aure bautar maza ne, domin a cewarta, maza da yawa na yin aure ne domin su samu masu yi masu bauta.
A kan haka ta yi kira ga mata da su rika gina kan su ta hanyar samar wa kansu sana'o'in hannu da sauran abubuwa masu muhimmanci.
Asali: Legit.ng

