Jami'an DSS Sun Cafke Mutum 5 na Kusa da Tsohon Gwamna kan Yunkurin Juyin Mulki
- Jami'an hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun cafke wasu na kusa da tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva
- Majiyoyi sun bayyana cewa an cafke mutanen ne yayin da ake ci gaba da shari'a kan yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
- Ana dai ci gaba da shari'an bayan an gurfanar da wasu mutane gaban kotu da ake zargi suna da hannu kan yunkurin juyin mulkin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja -Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun kama aƙalla mutane biyar da ke aiki kafadɗa da kafadɗa da tsohon karamin Ministan man fetur Timipre Sylva.
An gano cewa an kama su ne saboda zargin ɓoye bayanai game da inda Timipre Sylva yake, wanda ya shiga ɓuya tun lokacin da aka danganta shi da zargin wani yunƙurin juyin mulki.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta shigar da ƙara mai kunshe da tuhume-tuhume guda 13 a kan farar hula bakwai da ake alaƙantawa da yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
An gurfanar da wasu a kotu
Shida daga cikin waɗanda ake zargin da laifin yunkurin juyin mulkin, waɗanda rundunar sojojin Najeriya da hukumar DSS suka bincika, an zarge su da tsoratar da ‘yan ƙasa, da kuma ƙulla makarkashiyar korar gwamnatin dimokuradiyya, rahoton The Guardian ya nuna hakan.
Tuhume-tuhumen da aka shigar a kansu sun shafi cin amanar ƙasa, haɗin baki don kifar da gwamnati, haɗin baki don kitsa ta’addanci da sauran laifuffuka masu alaƙa da barazana ga tsaron ƙasa.
An bayyana Sylva, wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Bayelsa, a matsayin mutum na bakwai da ke gudun hijira tun watan Afrilun 2026 lokacin da aka gurfanar da sauran a gaban kotu, kuma ana yi masa shari’a ne ba ya nan a gaban babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja.
Meyasa aka cafke mutanen Sylva?
Yayin da yake ba da sabon bayani kan lamarin ba tare da bayyana sunansa ba, wani babban jami'i a cikin hukumomin tsaro ya bayanna cewa an gudanar da bincike kan ma’aikatansa guda biyar, waɗanda kuma na kusa da shi ne, kuma za a gurfanar da su nan ba da jimawa ba.
Majiyar ta yi bayanin cewa laifin nasu na iya zama mafi girma fiye da na Sylva saboda gazawarsu wajen bayyana inda yake da sauran bayanan da za su iya kaiwa ga kama shi.
“Sun kasa ba da haɗin kai ga masu bincike. Hakan na nufin su ma masu taimakawa ne, kuma masu haɗin baki ne a wannan yunkuri na adawa da dimokuradiyya. Ba da jimawa ba za su fuskanci shari'a a kotu."
- Wata majiya

Source: Twitter
DSS ta cafke wasu mutane
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an hukumar DSS sun cafke mutum biyar, da ake zargin suna da hannu a harin da aka kai wata makaranta a jihar Neja.
Daga cikin mutanen da aka kama har da wasu ‘yan ƙasar Nijar biyu, da ake zargi da safarar makamai ga ‘yan bindigan da suka kai hari makarantar.
Jami’an na DSS sun samu nasarar ƙwato tarin makamai masu yawa daga hannun mutanen da aka kama ciki har da kirar AK-47.
Asali: Legit.ng


