'Idan da Buhari Ya Kara Zama a Mulki, da Najeriya Ta Samu Ci Gaba': Abdulsalami
- Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ya yi magana game da mulkin marigayi Muhammadu Buhari da mataimakinsa a Najeriya
- Abdulsalami ya ce da gwamnatin Buhari da Tunde Idiagbon ta ci gaba da mulki fiye da watanni 20, Najeriya za ta fi samun ci gaba
- Ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta dawo da doka, tsari da kishin kasa, duk da suka da aka yi kan tsare mutane ba tare da shari'a ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ya bayyana tasirin gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari a Najeriya.
Abdulsalami ya bayyana cewa Najeriya na iya samun ci gaba idan da Buhari da Birgediya Tunde Idiagbon sun ci gaba da mulki fiye da watanni 20 da ta yi.

Source: Facebook
A babi na 10 na littafinsa mai suna Call of Duty: My Autobiography, Abdulsalami ya yi waiwaye kan jerin juyin mulkin da suka sauya tarihin siyasar Najeriya, cewar The Nation.
Abdulsalami ya yaba salon mulkin Buhari na farko
A cewarsa, duk da kura-kuran gwamnatin Muhammadu Buhari, ta samu nasarar dawo da da'a, kishin kasa da bin doka a lokacin da mutane da dama suka rasa amincewa da gwamnatin farar hula.
Ya ce gwamnatin Buhari da Idiagbon ta kawo sauyi mai yawa, inda ta bullo da shirye-shiryen tsaftar muhalli, tsara layuka a hukumomi da kuma karfafa bin dokokin jama'a.
Abdulsalami ya ce Buhari da Idiagbon mutane ne masu ladabi da bin ka'ida, kuma sun yi kokarin tabbatar da doka da oda tare da inganta kishin kasa tsakanin 'yan Najeriya.
Ya ce duk da kura-kurai, gwamnatin ta yi kokarin gyara matsalolin da suka dabaibaye kasa a lokacin, amma mutane da yawa sun dauke ta a matsayin mai tsauri.
Tsohon shugaban kasar ya yi imanin cewa idan gwamnatin Buhari ta samu karin lokaci, Najeriya za ta samu karin doka da oda fiye da yadda ake gani yanzu.
Abdulsalami ya kuma bayyana cewa sabanin yadda mutane da yawa suka yi zato, bai san komai ba game da juyin mulkin Agustan 1985 da ya hambarar da Buhari.

Kara karanta wannan
N70000 ta yi kadan: NLC za ta sake zama da Tinubu kan sabon mafi karancin albashi

Source: Facebook
Zargin da aka taɓa yi wa Abdulsalami
Abdulsalami ya kuma bayyana cewa an taba yi masa tambayoyi kan zargin yunkurin juyin mulkin Mamman Vatsa na shekarar 1986 saboda ya halarci wani taro da wasu daga cikin wadanda ake zargi suka halarta.
Ya ce daga baya an wanke shi bayan ya bayar da gamsassun bayanai ga kwamitin bincike na musamman da aka kafa domin binciken lamarin, cewar Punch.
Haka kuma ya tuna yadda ya tsallake shiga rikicin juyin mulkin Gideon Orkar na shekarar 1990 saboda yana kasar Saudiyya yana gudanar da Umrah lamarin ya faru.
Ya ce daga baya ya gano cewa Kyaftin Steve Ihile, wanda ya taba rokon ya yi wa Najeriya addu'a, na cikin wadanda aka kashe bayan juyin mulkin ya gaza.
Yadda Abdulsalami ya shawarci Obasanjo kan zaben 1999
Mun ba ku labarin cewa Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya ya bayyana yadda ya shawarci Olusegun Obasanjo game da tsayawa takara a zaben 1999.

Kara karanta wannan
Ran Rarara ya baci da aka soki Tinubu kan tsaro, ya zargi Davido da bata Najeriya
Tsohon shugaban mulkin sojan ya ce gwamnatinsa ba ta goyi bayan Obasanjo ba, duk da rade-radin cewa sun taimaka masa ya zama shugaban kasa .
Abdulsalami ya bayyana cewa ya sassauta ka'idojin rajistar jam'iyyu domin AD ta samu shiga, ta tabbatar da adalci da zaman lafiya a kasa.
Asali: Legit.ng
