"Da an Kai Shi Gidan Yari"; Fadar Shugaban Kasa Ta Jikawa Atiku Aiki kan Taba Tinubu
- Fadar shugaban ƙasa ta ce ƙoƙarin Atiku Abubakar na tayar da tsohon batun kwacen kadarorin Bola Tinubu a Amurka ba zai amfane shi ba
- Hadimin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce Atiku ya kashe dala miliyan 1.2 wajen ɗaukar hayar wani kamfani a Amurka
- Onanuga ya ce sake kawo zarge-zargen da aka yi amfani da su a yaƙin neman zaɓen 2023 ba zai ƙara wa Atiku damar cin zaɓen 2027 ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja – Fadar shugaban ƙasa ta ce ƙoƙarin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na sake tayar da batun shari'ar kwace kadarorin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Amurka ta hannun kamfabin ƙasashen waje, ba zai haifar masa da wani amfani ba.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis, 23 ga watan Yulin 2026, hadimim shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya ce tarihin Atiku a matsayin jami'in gwamnati bai ba shi dalilin neman goyon bayan 'yan Najeriya ba.

Source: Facebook
Bayo Onanuga wanda ya ke ba da shawara ga Shugaba Tinubu kan harkokin yada labarai da dabaru ya sanya sanarwar ne a shafinsa na X.
Onanuga ya kuma yi zargin cewa da ace Atiku ɗan ƙasar China ne, da tuni yana gidan yari saboda abin da ya kira laifuffukan da ya aikata kan al'ummar Najeriya.
Onanuga ya soki Atiku
A cewar Onanuga, tsananin burin Atiku na zama shugaban Najeriya ya sa ya yi watsi da ɗabi'un dattako, kamun kai da mutuncin da ake sa ran wani dattijon ɗan siyasa ya nuna.
Ya ce maimakon ya rungumi mutunci da natsuwar da suka dace da matsayinsa, Atiku na ci gaba da rage darajarsa ta hanyar kalamai marasa hankali da kuma matakan siyasa na neman mafita ta kowace hanya.
Onanuga ya ce abin mamaki ne yadda mutumin da ya shafe fiye da shekara 30 yana neman shugabancin Najeriya ya koma kai ƙarar shugaban ƙasar ga shugaban Amurka, Donald Trump, da kuma mambobin Majalisar Dokokin Amurka.
Batun shari'ar shekarar 1993
Sanarwar ta ce a sabon matakin da Atiku ya ɗauka, ta hannun wani kamfanin Amurka na miƙa koke ga Shugaba Donald Trump da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka kan wata shari'ar kwace kadarori ta farar hula da aka yi a shekarar 1993.
Onanuga ya ce an riga an kammala wannan shari'a tun da dadewa, kuma ba a taɓa samun hukuncin aikata laifi ko tabbatar da laifi a kanta ba.
Ya ƙara da cewa idan har Atiku ya iya kashe dala miliyan 1.2 wajen ɗaukar hayar kamfanin domin kai ƙarar Tinubu, ya kamata kuma ya fayyace matsayinsa na shari'a a Amurka.
A cewarsa, Atiku ya fito sosai a cikin badakalar cin hanci da ta shafi William Jefferson, lamarin da ya kai ga daure ɗan majalisar Amurka a gidan yari.

Source: Twitter
Shugaba Tinubu bai damu ba
Onanuga ya ce Shugaba Tinubu bai damu da abin da ya kira wasan kwaikwayon siyasar Atiku ba.
Ya kuma yi zargin cewa burin Atiku na zama shugaban ƙasa ba wai kawai yana da alaƙa da abin da ya kira "dadadden burinsa ba", har ila yau yana da nasaba da neman kariyar diflomasiyya da kuma kauce wa yiwuwar matsalolin shari'a a ƙasashen waje.
A ƙarshe, Onanuga ya ce sake fito da takardu da zarge-zargen da aka yi amfani da su a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023 ba zai inganta damar Atiku a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba.
Atiku ya bukaci Tinubu ya yi murabus
A wani labarin kuma, kun ji cewa Alhaji Atiku Abubakar ya bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus daga mukaminsa.
Atiku ya bukaci Tinubu ya yi murabus daga mukaminsa ne kan badakalar da ta dabaibaye batun ma'aikatar bogi ta PFIPC.
Asali: Legit.ng


