Najeriya da Wasu Kasashe 59 da Trump Ya Kakabawa Harajin Shigo da Kayayyaki

Najeriya da Wasu Kasashe 59 da Trump Ya Kakabawa Harajin Shigo da Kayayyaki

  • Amurka ta kakaba sabon haraji kan kayayyakin da ake shigo da su daga ƙasashe 60, ciki har da Najeriya
  • Najeriya za ta fuskanci harajin 12.5%, yayin da wasu ƙasashe za su biya 10% saboda hana kayayyakin da aka samar ta aikin tilas
  • USTR ta ce matakin ya biyo bayan bincike da ta gudanar tun watan Mayun 2026 tare da tattaunawa da gwamnatoci sama da 45

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

Amurka - Gwamnatin Amurka ta sanar da kakaba sabon haraji kan kayayyakin da ake shigo da su daga ƙasashe 60, ciki har da Najeriya, saboda abin da ta bayyana a matsayin gazawarsu wajen hana shigo da kayayyakin da aka samar ta hanyar aikin tilas.

Matakin, wanda Ofishin Wakilin Kasuwanci na Amurka (USTR) ya sanar a ranar Alhamis, ya tanadi harajin kashi 10 ko kuma kashi 12.5 bisa ɗari, gwargwadon yadda kowace ƙasa ta ɗauki matakan hana shigo da kayayyakin da aka samar ta hanyar aikin tilas.

Kara karanta wannan

An ja daga tsakanin Amurka da China kan haraji, kasar ta gargadi Trump

Donald Trump ya kakaba haraji kan Najeriya da wasu kasashe 59
Shugaban kasar Amurka Donald Trump da shugaban Najeriya Bola Tinubu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

USTR ta ce ta fara binciken ne tun watan Mayun 2026 kan manyan abokan hulɗar kasuwancin Amurka guda 60, inda ta karɓi fiye da ra'ayoyi 1,600 daga jama'a, ta saurari shaidu sama da 100, sannan ta tattauna da gwamnatoci fiye da 45 kafin yanke wannan hukunci, in ji rahoton Punch.

Amurka ta kakabawa kasashe 60 haraji

Najeriya na cikin ƙasashen da za su fuskanci harajin kashi 12.5 cikin ɗari.

Sai dai ƙasashen da USTR ta ce sun riga sun haramta ko kuma sun yi alƙawarin hana shigo da kayayyakin da aka samar ta hanyar aikin tilas za su biya harajin kashi 10 cikin ɗari kacal.

Wasu daga cikin ƙasashen da za su fuskanci harajin kashi 12.5 cikin ɗari sun haɗa da China, Rasha, Australia, Brazil, Masar, Saudiyya, Afirka ta Kudu, Hadaddiyar Daular Larabawa, Turkiyya da Vietnam.

Yayin da Canada, Birtaniya, Indiya, Pakistan, Malaysia, Bangladesh, Cambodia da Mexico ke cikin waɗanda za su biya harajin kashi 10 cikin ɗari.

Kara karanta wannan

Trump ya kara tsaurara matakan kasuwanci, ya laftawa Najeriya haraji

Kasashe 60 da aka kakabawa haraji

Ga cikakken jerin kasashe 60 da Amurka ta kakabawa harajin shigo da kayayyaki:

Kasashe

Haraji (%)

Algeria

12.5

Angola

12.5

Argentina

10

Australia

12.5

Bahrain

12.5

Bangladesh

10

Brazil

12.5

Cambodia

10

Canada

10

Chile

12.5

China

12.5

Colombia

12.5

Costa Rica

12.5

Dominican Republic

12.5

Ecuador

10

Egypt

12.5

El Salvador

10

European Union*

10

Guatemala

10

Guyana

12.5

Honduras

10

Hong Kong

12.5

India

10

Indonesia

10

Iraq

12.5

Israel

12.5

Japan*

12.5

Jordan

10

Kazakhstan

12.5

Kuwait

12.5

Libya

12.5

Malaysia

10

Mexico

10

Morocco

12.5

New Zealand

12.5

Nicaragua

12.5

Nigeria

12.5

Norway

12.5

Oman

12.5

Pakistan

10

Peru

12.5

Philippines

12.5

Qatar

12.5

Russia

12.5

Saudi Arabia

12.5

Singapore

12.5

South Africa

12.5

South Korea*

12.5

Sri Lanka

10

Switzerland*

12.5

Taiwan*

10

Thailand

12.5

The Bahamas

12.5

Trinidad and Tobago

10

Turkey

12.5

United Arab Emirates

12.5

United Kingdom

10

Uruguay

12.5

Venezuela

12.5

Vietnam

12.5

Kara karanta wannan

Idon Trump ya koma kan kadarorin Iran da ke Amurka, ya fara kai masu barazana

Trump ya laftawa Najeriya haraji

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Amurka ta kakaba harajin 12.5% kan kayayyakin da ake shigowa da su daga Najeriya saboda zargin rashin dakile kayayyakin da aka samar da aikin tilas.

Sabon matakin ya shafi kasashe 60, inda Amurka ta ce ba su kafa ko aiwatar da dokokin hana shigo da kayayyakin da aka samar ta hanyar aikin dole ba.

Hukumar Kasuwancin Amurka ta ce matakin na daga cikin kokarin gwamnatin Donald Trump na yaki da amfani da aikin tilas a harkokin kasuwanci na duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com